Shinkafa da miya da salad2

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Miya idan ta soyu tafi dadi gaskia

Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa kofi biyu
  2. _____________
  3. Kayan miyar
  4. Tattasai gwada8
  5. Albasa babba2
  6. 8Tumatur guda
  7. Tumatur na leda guda1
  8. Attarugu guda6
  9. Maggi guda10
  10. Nama rabin kilo
  11. cokaliKayan kamshi rabin
  12. Tafarnuwaguda8
  13. Mai rabin kofi
  14. cokaliCurry rabin
  15. __________________
  16. Kayan hadin salad
  17. 10Latas guda
  18. Albasa rabi
  19. Tumatur biyu
  20. Cucumber rabi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki daura ruwa a tukunya idan ya tafasa sai ki wanke shinkafa ki zuba ki rufe ki bata minti 30 tayi sai ki tace ta da abun tace shinkafa

  2. 2

    Sai ki wanke naman ki kisa masa kayan kamshi kisa tafarnuwa kisa maggi ki zuba ruwa ki yanka albasa ki daura akan wuta ki basa minti 20 har sai ruwan ya kusa tsanewa sai ki sauke

  3. 3

    Ki jagaga albasar ki da attarugu da tattasai da tumatur ki aje gefe bayan nan sai ki daura mai a tukunya ki yanka albasa idan ya fara zafi ki fasa tumatur din leda ki zuba ki soya shi

  4. 4

    Bayan nan sai ki kawo sauran kayan miyar da kika jajaga koh kika nika sai ki zuba ciki ki cigaba da soya su sai ki kawo maggi da kayan kamshi da curry ki zuba ki cigaba da soyawa bayan man ya fara fitowa sai ki kawo nama ki zuba ki motsa ki rufe ki bata minti biyar ta kara soyuwa shikenan miyar ki ta hadu

  5. 5

    Sai ki yanka salad dinki da su Albasa da tumatur da cucumber dinki sai ki jera su cikin plate shikenan sai ci 😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

sharhai

Similar Recipes