Taliya da miyar jajage da salad

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Na gano cewar miyar jajage tafi dadi aci ta da taliya

Taliya da miyar jajage da salad

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Na gano cewar miyar jajage tafi dadi aci ta da taliya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Saliya rabin leda
  2. Tumatur na leda daya
  3. Albasa babba biyu
  4. Tattasai6
  5. Attarugu3
  6. Mai rabin kofi
  7. Maggi gud10
  8. Nama rabin kilo
  9. Salad slice8
  10. cokaliCurry rabin
  11. Tafarnuwaguda5
  12. cokaliKayan kamshi rabin

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki daura ruwa akan tukunya idan ya tafasa sai ki fasa taliya ki karyata ki zuba kina iya zuba dan gishiri idan kina so

  2. 2

    Bayan nan sai ki rufe ki barta ta dahu zuwa minti 30 sai ki sauke ki tace ta ki zuba ruwan sanyi ki dauraye kar ta dunk'ule

  3. 3

    Miyar kuma zaki daura nama kisa masa Maggi da kayan kamshi da albasa ki barshi ya dahu zuwa minti 20

  4. 4

    Bayan ya dahu sai ki sauke ki daura mai a tukunya ki yanka albasa sai ki kawo tumatur din leda dinki ki zuba ki soya Shi idan ya soyu sai ki kawo kayan miyar ki da kika jajaga ki zuba ciki ki cigaba da soyawa bayan minti goma ki kawo maggi ki zuba

  5. 5

    Ki kawo curry ki zuba kisa sauran kayan kamshin ki cigaba da soyawa Idan ta kusa soyuwa sai ki zuba nama ki motsa ki rage wuta ki barta ta kara soyuwa shikenan sai ki sauke kisa a faranti

  6. 6

    Sai ki yanka salad dinki Wanda kika wanke

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

sharhai

Similar Recipes