Pizza

Augie's Confectionery
Augie's Confectionery @Augiee01
Sokoto

Wanan hadin pizza ana yin sa ba da cheese ba.Na hada shi musamman saboda mama na da ba ta son cheese.Nayi amfani da ketchup a maimakon pizza sauce saboda tana son ketchup sosai amma zaku iya amfani da pizza sauce ko stew.

Pizza

Wanan hadin pizza ana yin sa ba da cheese ba.Na hada shi musamman saboda mama na da ba ta son cheese.Nayi amfani da ketchup a maimakon pizza sauce saboda tana son ketchup sosai amma zaku iya amfani da pizza sauce ko stew.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2Flour kofi
  2. Mai cokali babba 3 cokali 1 na shafawa akan dough
  3. 1Yeast cokali babba
  4. 1Gishiri cokali karami
  5. 1Sugar cokali karami
  6. Ruwa mai dumi cup 3/4
  7. 3Tomatur
  8. 1Tattasai ja
  9. 1Tattasai green
  10. 1Albasa
  11. Lettuce
  12. Nama agashe
  13. Maggi
  14. Curry
  15. Ketchup
  16. 1Egg babba

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko za ki auna flour,yeast,sugar da gishiri ackin roba

  2. 2

    Sai ki mosa su hade

  3. 3

    Sai ki sa mai cokali babba 2,sai ki murza cikin hadin flour

  4. 4

    Sai ki zuba ruwa mai dummi ki kwaba flour sai ta hadu.Ki buga na minti biyar sai tayi laushi.Sai a sa brush ko hanu a shafa mai ackin roba da saman dough din sai a rufe a bar shi yayi resting na minti goma

  5. 5

    Ki wanke kayan lambu ki yanka ya da kike so,shima agashen a yanka a ajiye a gefe

  6. 6

    Bayan minti 10,sai a dauko dough din a barbada flour akan table,sai a murza da roll pin daidai baking sheet na ki ko kuma kiyi rolling round.Sai a shafa mai a pan din, a barbada flour sai a dora dough a kan pan.Za ki iya sa wuka ko scissor kiyi trimming edges din.sai ki shafa mai a saman dough,wannan zai hana masa jika da kayan lambun da za a sa a saman

  7. 7

    Sai a matsa ketchup a shafa a saman,a sa lettuce,tattasai,tomaur,albasa da agashen

  8. 8

    Sai ki fasa kwai,ki sa masa gishiri,curry da maggi ki kada,sai ki zuba a sama

  9. 9

    A gasa cikin oven na minti 15

  10. 10

    Ayi serving

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Augie's Confectionery
rannar
Sokoto
I'm a culinary artist/pastry chef,love to explore more in the culinary world.I love baking or let me just say it's my profession.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes