Peanut Burger

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Na Dade banci ta ba sai gashi da nayi da kaina yayi dadi sosai. Duk wanda ya ci sai ya yaba

Peanut Burger

Na Dade banci ta ba sai gashi da nayi da kaina yayi dadi sosai. Duk wanda ya ci sai ya yaba

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Gyadar miya Kofi 1 da rabi
  2. Sukari Rabin kofi
  3. 4Kwai guda
  4. Filebo karamin cokali 1
  5. Fulawa yanda zata isa
  6. Baking powder karamin cokali 1
  7. Gishiri Dan kadan
  8. Madara cokali 1
  9. Man suya

Cooking Instructions

  1. 1

    A gyara gyada a tsince dattin a tabbatar ya fita, a cire wadanda suka bare da kuma kananan ya zama gyadar guda ce me kyau kuma.

  2. 2

    A FASA kwai a roba a saka sukari, madara, Baking powder da Dan gishiri a juya sosai har ya hade, a saka filebo ma a juya sai a ajiye a gefe

  3. 3

    A sami babbar roba sosai ko Nace baho a juye gyadar a ciki, sai a Dan zuba hadin kwan a juya Idan koina yaji sai a barbada fulawa aita juyawa da robar ana yi ana rarraba wanda ya hade.

  4. 4

    Haka za a maimaita har sai anga gyadar ta rufe babu alamar ana ganin gyadar.

  5. 5

    Sannan a dora mai akan wuta Idan ya fara zafi sai a kwashe albasar a dunga zuba gyadar ana soyawa ana jujjuyawa don koina ya zama kala daya.

  6. 6

    Idan ta soyu sai a kwashe a kwalanda a barta ta tsane. A barta ta sha iska tafi dadi.

  7. 7

    An kammala.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
on
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Read more

Comments

Similar Recipes