Tsami gaye

mumeena’s kitchen
mumeena’s kitchen @000000h
kano nigeria

#Alawa tsami gaye yana da matukar dadi kuma yana daga cikin alawowin gargajiya tun muna yara muke siyen sa muna sha ban taba yi ba sai dai n siya yau Allah yyi n gwada shi kuma naji dadin shi don har yafimin n siyarwa dadi saboda nasa fulebo a nawa

Tsami gaye

#Alawa tsami gaye yana da matukar dadi kuma yana daga cikin alawowin gargajiya tun muna yara muke siyen sa muna sha ban taba yi ba sai dai n siya yau Allah yyi n gwada shi kuma naji dadin shi don har yafimin n siyarwa dadi saboda nasa fulebo a nawa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

20mintuna
5 yawan abinchi
  1. 2Garin kwalba kofi
  2. 1 1/2Sugar kofi
  3. 1 tspKalar abinchi pink
  4. 1/2 tspVanilla fulebo
  5. 1/2 cupRuwa

Umarnin dafa abinci

20mintuna
  1. 1

    Ga abubuwan d muke bukata domin yin shi wannan tsami gayen

  2. 2

    Da farko xaki xuba sugan ki a tukunya sai ki xuba ruwan ki juya

  3. 3

    Sai ki dora akan wuta ki barshi har y narke

  4. 4

    Bayan y fara narkewa sai ki xuba kalar ki juya

  5. 5

    Sai ki xuba vanilla dinki sai ki kashe wutar ki sauke shi kasa

  6. 6

    Sai ki kawo garin kwalba ki xuba ki juya shi har y hade sugan d garin kwalbar

  7. 7

    Sai ki juye shi a kan parchments takarda ko kuma ki juye a kan leda

  8. 8

    Sai ki shafa mai a jikin muciyar ki ki dan murza shi ma’ana ki fakada shi

  9. 9

    Sai kisa wuka ki yanka shi a tsaye sannan a kwance

  10. 10

    Nan gashi bayan kin gama yayyankawa

  11. 11

    Shikkenan kin gama asha dadi lpy

  12. 12

    Gashi bayan na chanja mishi bagirahun

  13. 13

    Hmm dadi ba’a magana

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mumeena’s kitchen
rannar
kano nigeria

sharhai (3)

Hauwau Kamilu Aminu
Hauwau Kamilu Aminu @jidderh_cuisine
Naga yyi kyew sosai Amma Dan Allah sai naga kaman da mai a jikinshi

Similar Recipes