Dublan

mumeena’s kitchen
mumeena’s kitchen @000000h
kano nigeria

A gaskiya ina son dublan sosai saboda garas garas din d yake a baki sannan kuma ga xakin suga hade d dan tsami tsamin lemo tsami nakasance tun a da in ankawo gara yana daga cikin abinda yake burgeni ga wata yar hanya yar uwa d xaki bi domin ki kawata dublan dinki ki bashi shape mai kyau kudai kawai ku gwada #Dublan

Dublan

A gaskiya ina son dublan sosai saboda garas garas din d yake a baki sannan kuma ga xakin suga hade d dan tsami tsamin lemo tsami nakasance tun a da in ankawo gara yana daga cikin abinda yake burgeni ga wata yar hanya yar uwa d xaki bi domin ki kawata dublan dinki ki bashi shape mai kyau kudai kawai ku gwada #Dublan

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mintuna
3 yawan abinchi
  1. 1Fulawa kofi
  2. Sugar 1/8 kofi
  3. Mai cokali 1
  4. 1/3 cupRuwa
  5. Abubuwan d kike bukata in xaki dafa suga
  6. 1Sukari kofi
  7. Lemon tsami rabi
  8. Ruwa 1/3 kofi

Umarnin dafa abinci

30mintuna
  1. 1

    Da farko ga abubuwan d xamu kwaba shi wannan dublan

  2. 2

    Xaki tankade fulawar ki ki xuba a kwano sai ki xuba duka mahadanki ki juya ki xuba ruwa ki kwaba shi har y hade jikinsa

  3. 3

    Sai ki barbada fulawa a inda xaki murza saboda kar y makale ki murza fulawar ki har tayi fadi ana sonta kalai kalai saboda kar yyi tuwo ciki shi dublan garas garas ake so yyi

  4. 4

    Bayan kin gama murzawa sai ki sa Mai circle ki ciccire zagayen

  5. 5

    Sai kisa hannun ki a gefen fulawar taki ki matse shi kmr haka

  6. 6

    Haka xakiyi har ki gama

  7. 7

    Sai ki dora mai a wuta in yyi xafi sai ki saka dublan dinki in bangare daya yyi sai ki juya daya bangaren m yyi

  8. 8

    Bayan y soyu sai ki tsane shi a mataci

  9. 9

    Sai ki dawo kan suganki ki xuba shi a tukunya ki xuba ruwan ki a ciki sai ki matse lemon tsami ki barshi y dahu

  10. 10

    Bayan y dahu sai ki sauke sai ki kawo wannan dublan dinnan naki ki sa aciki ki juya daya bangaren shima sai ki barbada kantu akai

  11. 11

    Shikkenan kin gama

  12. 12

    Gaskiya naji dadinshi sosai 😋😋

  13. 13

    Hmmm😍

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mumeena’s kitchen
rannar
kano nigeria

sharhai

Similar Recipes