Parcel gift samosa

Yakudima's Bakery nd More
Yakudima's Bakery nd More @cook_17249948
Kano

Anayintane saboda abu na musamman kamar karbar baki ko ayiwa oga dadai sauransu

Parcel gift samosa

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Anayintane saboda abu na musamman kamar karbar baki ko ayiwa oga dadai sauransu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2 cupflour
  2. 1 tspsalt
  3. 1 tspthyme
  4. 3 tbspoil
  5. water asreguired
  6. red color
  7. minced meat
  8. onions & garlic
  9. patotaes
  10. 1 tbspcorn flour
  11. maggi & salt
  12. curry, cumin & black pepper

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki kankade flour kizuba mata salt,oil da thyme seki kwaba ki rufeta ki ajiyeta tayi kamar minti 15 ko 20

  2. 2

    Zaki dafa potatoes da carrot daban gashi nan kamar haka anyanka andafa gasu nan a kwano.zaki daura pan akan wuta ki zuba masa oil idan ya dau zafi seki saka masa garlic da onions da attaruhu ki dan soyasu kamar na minti 5 seki zuba minced meat kisa maggi salt da curry da cumin,black pepper

  3. 3

    Zaki juyashi sosai seki rufeshi kibarshi kamar minti 10 ko 15 seki bude zakiga ruwa yafito jikinsa sekiyita juyawa harsai ruwan ya kamejikin naman seki zuba masa carrot da potatoes kijuya seki kwaba corn da ruwa kadan ki zuba akai ki juya ki barshi kamar minti 4 ko 5 seki sauki ki ajiye ta huce kafin kizo amfani dashi

  4. 4

    Gashi nan na juye shi

  5. 5

    Bayan minti 20 gashi nan na dauko kwabina na kuma kwabata na gutsiri yar kadan na saka mata red color zan kwabata sosai sena murzata na yankata kamar haka

  6. 6

    Gashi nan ita kuma wadda bansawa kala ba narabata gida 4 wacce na gutsiri yar kadan ajikinki zan ajiye.zan murzata kamar haka sena zuba mata nama kamar haka

  7. 7

    Gashi nan na kwaba fulawa da ruwa kamar kwabin wainar fulawa, bayan na zuba nama zanninke kamar haka sena shafa wannan kwababbiyar fulawar gashi nan kamar haka

  8. 8

    Zandauko jan layi daya sena shafa masa ruwa ajiki sena daura kamar haka sena juya dashi ta bayama se kuma dauko wani na kuma yimasa kmr yanda nayi wancan gashi nan kamar haka

  9. 9

    Sena dauko wannan gutun dana gutsira na dan murzashi kamar haka sena yankashi na maidashi * sena shafa ruwa na daura akai

  10. 10

    Sena kuma gutsirar jar yar kadan na lallayata na zafa mata ruwa na daurata akai gashi nan kamar haka.haka suma sauran zanyi musu idan na gama sena daura mai a wuta nayi kasa da wutar idan man ya dau zafi seki saka nasuya

  11. 11

    Alhamdulillah mungama parcel gift samosa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yakudima's Bakery nd More
rannar
Kano
I love exposing new delicacies
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes