Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 3kofi shinkafar tuwo
  2. 1/2kofi yoghurt ko nono
  3. 1 cokalisukari
  4. gishiri kadan
  5. 4kofi mai
  6. miyar taushe
  7. 3albasa
  8. 3tumatur
  9. 4attaruhu
  10. 3tattasai
  11. 6maggi
  12. 1/2kofi mai
  13. alayyahu
  14. kabewa
  15. 1kofi gyada
  16. ruwa yadda zai ishe ki
  17. kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A jika danyar shinkafa/shinkafar tuwo,a barta ta kwana

  2. 2

    Washegari a wanke a kai markade

  3. 3

    Idan an kawo a zuba yoghurt ko nono,a juyaa sosai,sai a ajiye a rana a barta ta tashi,idan ya tashi a zuba gishiri kadan da sigar cokali daya a juta sosai

  4. 4

    A dora tanda a wuta a zuba mai cokali daya a kowanne rami,sannan a barshi yayi zafi,a zuba ludayi daya na kullin waina a kiwanne rami,a saka wuta kadan a bari bayan ya soyu,udaan ya soyu a juya dayan bayan ya soyu sannan a kwashe,haka za'a yi tayi har a gama.

  5. 5

    A gyara kayan miya a wanke a markada,a dora a wuta a dafa,sannan a wanke

  6. 6

    A fereye kabewa a wanke a dafa,a markada ko a niqa

  7. 7

    A gyara gyada sannan a daka ta

  8. 8

    A gyara alayyahu,a wanke da ruwan gishiri,sannan a kara wankewa sosai da ruwa,a yanka shi

  9. 9

    A zuba mai a cikin tukunya a dora a wuta sannan a zuba kayan miyar a soya,a zuba kabewa da gyada da maggi da kayan kamshi a zuba mishi isashen ruwa a barshi ya dahu sosai,idan ya gyadar ta dahu ruwan ya janye sai a zuva alayyahu,a barshi minti 2 a sauke.Miyar taushe wadda ake ci da waina ko sinasir ba'a yinta da kauri sosai,an fi son ta ruwa-ruwa.

  10. 10

    Aci dadi lfy.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
M's Treat And Confectionery
rannar
Zoo road,Kano,Nigeria
A Food biochemist by profession and a food lover by passion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes