Ring Samosa II

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

Sakamakon korafi na followers Dina akan rashin sa step by step pictures shiyasa na sake Yi muku domin kaunata agareku masoyana kuci gaba da kasancewa da MEENAT KITCHEN akoda yaushe

Ring Samosa II

Sakamakon korafi na followers Dina akan rashin sa step by step pictures shiyasa na sake Yi muku domin kaunata agareku masoyana kuci gaba da kasancewa da MEENAT KITCHEN akoda yaushe

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mintuna
1 yawan abinchi
  1. Flour Kofi daya
  2. Mai babban cokali 2
  3. cokaliSukari rabin karamin
  4. cokaliGishiri kwatan karamin
  5. Maggi kadan
  6. fillings
  7. Minced meat
  8. Attarugu da albasa
  9. Maggi da kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

30mintuna
  1. 1

    Dafarko Zaki hada ingredients dinki na dough ki kwaba soft dough ki rufeshi ya Dan sarara na mintuna 10-15

  2. 2

    Kafin flour dinki tayi saiki Dora namanki a wuta kisa Maggi da albasa da kayan kamshi ki tafasashi idan ya dahu saikisa attarugu da dan Mai ki soya sama-sama

  3. 3

    Saiki dawo kan dough dinki kirabashi 3 saiki dauki daya ki murzashi da fadi saiki yanke gefe da gefe ya baki 4 kwana yaxama square kenan

  4. 4

    Saiki zuba nama a sama ki shafa kwabbabiyar flour saiki rufe naman saiki dauki wuka ko pizza cutter ki yanka a tsaye

  5. 5

    Saiki kuma shafa kwabbabiyar flour a karshe sai nade kamar tabarma

  6. 6

    Saiki lankwasata kamar ring kisa kwabbabiyar flour a karshe ki hade bakin duka biyun ki mannesu a tare

  7. 7

    Kinga yanda zai zama saikiyi yiwa sauran ma haka idan kin gama saiki Dora Mai a wuta idan yayi zafi ki soya

  8. 8

    Kisoyashi harsai yayi golden brown saiki kwashe ki tsanesa. Shikenan kin gama

  9. 9

    Enjoy

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

sharhai (11)

Halima Abdullahi
Halima Abdullahi @Hac_1988
Salam,ya azumi.please sis no need in Dan gasa flour din kar taki soyuwa ciki.

Similar Recipes