Homemade milk popcorn

mumeena’s kitchen
mumeena’s kitchen @000000h
kano nigeria

A gaskiya ina matukar son popcorn hakan yasa nake yinsa a gida b sai n siyo b

Tura

Kayan aiki

4 yawan abinchi
  1. 1 cuppopping corn(ta yin popcorn daban take)
  2. 2 tbspButter
  3. 1/2 cupSugar
  4. 2 cupsMilk

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko xaki narka butter dinki a tukunya Sai ki zuba popping corn dinki ki juya sai ki rufe tukunyar ki ruff

  2. 2

    A hankali xakiji kara yana farfacewa Sai ki dinga dan girgixa tukunyar taki a haka har y gama popping

  3. 3

    Nan gashi bayan y gama popping

  4. 4

    Sai kiyi melting wata butter din ki xuba a kai ki juya

  5. 5

    Sai ki xuba madarar ki d sugar ki juya sosai xakiga madarar ta kama jikinsa sosai Sai ki sauke

  6. 6

    Shikkenan kin gama

  7. 7

    Gaskiya akwai dadi in kinayi a gida shikkenan kin huta d siyan n titi

  8. 8

    Wannan itace masarar popcorn daman take d normal masara ita a dan mulmule take

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mumeena’s kitchen
rannar
kano nigeria

sharhai (4)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
@000000h irin gugurun nan nikeso ya soyu in samu da dare shikenan 😋😋

Similar Recipes