Kitsattsen dublan

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

#FPPC
Naga wannan girki tun wajen watanni 9 baya a wajen princess amrah lkcn ana cikin gasar dublan ya bani sha'awa amma sai nk jin kmr zai bani wahalar yi😩sai ynx na tattara qarfin gwiwar gwadawa......gashi dai bai samu wani hoton kirki ba amma muna godiya da gudummawarta garemu❤💥

Kitsattsen dublan

#FPPC
Naga wannan girki tun wajen watanni 9 baya a wajen princess amrah lkcn ana cikin gasar dublan ya bani sha'awa amma sai nk jin kmr zai bani wahalar yi😩sai ynx na tattara qarfin gwiwar gwadawa......gashi dai bai samu wani hoton kirki ba amma muna godiya da gudummawarta garemu❤💥

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40 mins
5 yawan abinchi
  1. Kofi uku na fulawa
  2. Cokaliuku na mai
  3. Sugar(yadda ake son zaqi)
  4. Madara cokali biyu
  5. Ruwa (yadda zai isa)
  6. Mai(don suya)
  7. Kwalliyan dublan
  8. Kofi daya da rabi na sukari
  9. Cokalidaya na lemon tsami
  10. Rabin kofi na ruwa

Umarnin dafa abinci

40 mins
  1. 1

    A cikin kwano a zuba flour,sugar,madara da mai,sai a zuba ruwa(da kadan kadan)har sai yayi,ya dan fi kwa6in cincin saki

  2. 2

    Ayi amfani da leda a rufe kwa6in a bashi minti 5 ya saki jikinshi,sai a dauko shi murzashi da fadi sosai,ayi amfani da abin yanka pizza a cire gefe da gefenshi ya koma fasalin murabba'i...(rectangle),sai a qara amfani da abin yankan a qara yayyanka su a tsaye

  3. 3

    Sai a ware yanka tara a kaM qarshensu a matsesu tare,sai a rabashi gida uku daga sama a mishi kitso(kalba) in an kai qarshen kitson sai a kamo farko da qarshen a hadesu waje daya(za a iya kwa6a fulawa a shafa a qarshen saboda ya zauna da kyau).

  4. 4

    Ga wani samfurin kuma da shi a wajen maryama's kitchen na gani,bayan an gama kwabin an murza,sai ayi amfani da kofi ko murfi mai fasalin da'ira a ciccire irin fasalin,sai a saka hannu a tsakiyan a matse

  5. 5

    Sai a daura mai a kan wuta (kar a barshi yy zafi sosai)sai a soya.Don hada kayan kwalliya kuma sai a daura tukunya kan wuta a zuba sukari da ruwa a barshi ya tafasa sosai har ruwan ya tsoste ya dan fara canza kala kadan sai a sauke a zuba ruwan lemon tsami,in ya huce sai a riqa tsumbula dublan din a ciki ko ina ya samu sai a tsamesu a barbada habbatus sauda a kai👋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes