Kayan aiki

  1. 4 cupsWaken soya
  2. 1/8 cupManja
  3. 1+1/2 tbsp Dan tsami+1 cup na ruwa ki hada
  4. Kanwa(ungurnu)
  5. Kayan aiki
  6. Mataci
  7. Roba mai fadi
  8. Tukunya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara waken soyar ki,ki tsince datti da tsakuwa,sai ki wanke.Zaki saka kanwar a waken sai ki kai markade.(Ba sai kin jika waken ba,da kin wanke zaki hada da kanwa a markado miki).

  2. 2

    Idan aka markado zaki zuba manja ki juya.(Amfanin manja saboda dusar waken ta fita sumul).

  3. 3

    Zaki gyara matacin ki sai ki tace wannan markaden ki ringa kara ruwa har ki fitar da madara mai kyau.

  4. 4

    Zaki juye madarar a tukunya mai girma ki kunna wuta.

  5. 5

    Da zarar tayi zafi sai ki zauna a kusa dan karta zube,zaki ga ta tafasa kamar haka.Sai ki fara tsiyaya dan tsaminki da kika hada da ruwa.(Ba'a juyawa da kansa zai ringa hadewa).

  6. 6

    Nan da nan zaki ga yana dunqulewa kamar yanda yake a hoton,sai ki barshi ya ci gaba da haduwa har ta hade,zaki ga ruwan ya koma garai garai,awarar kuma tana hadewa.

  7. 7

    Zaki kuma tacewa a mataci ki matse sosai.

  8. 8

    Zaki daure matacin ki ajiye shi dan ruwan tsane.Ba sai kin saka abu mai nawi ba,kawai idan kika murde matacin shike nan,idan ruwan ya daina fita sai ki kwance.

  9. 9

    Ga awara ta hadu.

  10. 10

    Zaki yanka ki shafeta da gishiri ki soya,ko ki saka ta a fridge.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Jahun's Delicacies
rannar
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Kara karantawa

sharhai (7)

Sarah Isaac
Sarah Isaac @Sarahrecipe
Dan Allah ba kowa su ka iya hausa ba, could u mk it more explanatory in English fr dose dat don't understand or can't read hausa , coz u do good in ur explaination tnx

Similar Recipes