Kayan aiki

  1. Waken suya
  2. Dan tsami
  3. Attaruhu
  4. Albasa
  5. Dandano
  6. Gishiri
  7. Mai
  8. Kwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaa gyara waken akai nika, nikan yayi laushi sosai

  2. 2

    Bayan an nika sai a kara ruwa a taceshi, sai a dora akan wuta a rufeshi

  3. 3

    Da ya tafaso sai ana zuba ruwan dan tsami(dama an rigada an jika)in yayi sai a rufe tadan dahu sai asa abin kwada a kwashe a zuba a abin tata a matse sai a bude a zuba dakakken attaruhu da albasa da 'dan ruwan Magi a kuma matsewa

  4. 4

    Inta dunkule duka sai a yayyanka

  5. 5

    A soya a ruwan kwai

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Rahinerth Sheshe's Cuisine
rannar
Kano @Danladi Nasidi Housing Estate.
Tun ina yarinya na taso da kaunar girki da sarrafa Shi kuma mahaifiya ta tabani goyon baya ta hanyar koyamin
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes