Kayan aiki

  1. Awara(danya)
  2. Cabbage
  3. Carrots
  4. Albasa
  5. Koren tattasai
  6. Jan tattasai
  7. Attaruhu
  8. Kayan kamshi
  9. Kayan dandano
  10. Timatir na leda
  11. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki shafe awarar da gishiri,sai ki soya a mai.

  2. 2

    Zaki jajjaga attaruhu,ki yanka albasa da timatir na leda ki soya a mai,hade da kayan kamshi dana dandano.

  3. 3

    Zaki zuba ruwa kadan dan ana so yayi kuri.

  4. 4

    Zaki gurza karas,ki yanka cabbage,koren tattasai da jan tatyasai dukka kananan yanka zakiyi,ki zuba a ciki,ki basu minti 3 sai ki kashe wutar.

  5. 5

    Zaki samu mazubi mai zurfi ki juye awarar da kika soya,ki zuba mata wannan miyar da kikayi akai ki juya.

  6. 6

    Dadi dai ba'a magana.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Jahun's Delicacies
rannar
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes