Tura

Kayan aiki

  1. Allayyaho
  2. Yakuwa
  3. Kayan Miya
  4. Kayan dandano
  5. Kayan kamshi
  6. Gyada
  7. Manja

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko uwar gida Zaki yanka allayyaho da yakuwa kanana sannan ki wanke su

  2. 2

    Ki jajjaga kayan miyan ki sannan ki daka gyadan ki yayi laushi

  3. 3

    Ki daura manja a tukunya ki yanka albasa ya soyu sannan ki sa kayan miyan

  4. 4

    Ki dauko dakakken gyadanki ki zuba akan kayan miyan ki gauraya su soyo nadan wani lokaci sannan kisa ruwa bame yawa ba sbd miyar tayi kauri

  5. 5

    Sannan kisa kayan dandanon ki Dana kamshi

  6. 6

    Idan ya tafasa ya nuna se kisa yakuwan sannan kisa kanwa sbd rage tsamin idan yakuwan yadau nunan se kisa allayyaho

  7. 7

    Ki barshi ya nuna na Dan wani lokaci sannan ki sauke aci dadi lfy

  8. 8

    Zaki iyaci da biski,tuwan shinkafa
    Nide nawa da cous cous zanci😋
    Ki biyoni Dan ganin yadda Zan dafa couscous dina

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
HAJJA-ZEE Kitchen
HAJJA-ZEE Kitchen @hajjazee3657
rannar
I really love cooking,baking and more 🥰😍
Kara karantawa

Similar Recipes