Tuwon shinkafa da miyar kuka

Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744

Miyar kuka na da dadi musamman in Tasha nama da daddawa#GARGAJIYA

Tuwon shinkafa da miyar kuka

Miyar kuka na da dadi musamman in Tasha nama da daddawa#GARGAJIYA

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafar tuwo kwata
  2. Ruwa
  3. Kayan miya
  4. Mai
  5. Maggi
  6. Nama
  7. Daddawa
  8. Kuka
  9. Wake
  10. Citta,tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki gyara shinkafarki ki wanketa,ki Dora ruwa a wuta har Sai ya tafasa ki kawo shinkafarki ki zuba ki rufe kinayi kina Kara ruwa har Sai tayi laushi sosai.

  2. 2

    Ki sauke tukunya kasa Kisa muciya ki tuka tuwon har Sai yayi sumul,ki maida kan wuta ki bari ya Kara turara.

  3. 3

    Saiki Sami roba ki sa Mai kadan kina dauko tuwon kina sawa a robar kina mulmulawa harki gama.

  4. 4

    Miyar kuka
    Ki wanke namanki ki yanka albasa tafarnuwa citta ki Dora a wuta ki tafasa.

  5. 5

    Ki kawo kayan miyarki ki zuba ki kawo daddawa da Kika dakata ki zuba da wake,Zaki iya hada daddawa da wake waje Daya ki dakasu.ki zuba Maggi mai da gishiri ki rufe harsai kin farajin kamshin daddawa.

  6. 6

    Saiki kawo kukarki ki kada a ciki ki bari ta dahu.Anacin wannan miyar da tuwon dawa,tuwon gero da kowane irin tuwo da kike so

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744
rannar
Ina kaunar girki musamman snacks da Kuma Miya kala kala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes