Gashasshen kifi

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya da rabi
2 yawan abinchi
  1. Kifi 1
  2. Lemon tsami 2
  3. Kayan kamshi
  4. tafarnuwaCitta da
  5. Sinadarin dandano 4
  6. Attaruhu 5
  7. albasa 1
  8. Man gyada

Umarnin dafa abinci

Awa daya da rabi
  1. 1

    Da farko uwar gida zata samu kifinta ta ta gyara ta cire kayan cikin sai ta wankeshi tas da ruwa da lemon tsami ta ajiyeshi gefe.

  2. 2

    Sai ta samu kwano ta zuba mai da dakakken citta da tafarnuwa da kayan kanshi tasa sinadarin dandano.

  3. 3

    Sai ta samu hadin ta zuba kan kifin ta shafawa ko ina har cikin kifin ta tabbatar ko ina yaji sai ta sa a fridge kamar na minti arba,in.

  4. 4

    Ta dan saka ruwa,sai tabar miyar ta soyu tanayi tana juyawa.

  5. 5

    Daga zata ciroshi tasa a mazubi sai ta juye ragowar miyar akai shikkenan kifin mu yayi.

  6. 6

    Bayan nan a kasko zata saka man gyada sai ta kawo albasa ta saka ta dan jujjuya sai ta attaruhun ta da ta jajja ta sa kayan kamshi da sinadarin dandano,

  7. 7

    Daga nan zata ciro kifin daga firji ta bude tsakiyan ta debi wannan miyar albasan ta zuba a cikin kifi sai ta dora akan abin gashi ta gasashi na tsawon minti 30.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Abk cuisines
Abk cuisines @Nawal12_
rannar

sharhai

Similar Recipes