Farfesun kifi

Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜 @fatumar6855
Zaria City, I'm Married💞💞💞

Farfesu na da muhimmanci ajiki sosai, shiyasa Ina kokarin yinsa domin gina jikin iyalina.

Farfesun kifi

Farfesu na da muhimmanci ajiki sosai, shiyasa Ina kokarin yinsa domin gina jikin iyalina.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti sha biyar
mutum hudu

Umarnin dafa abinci

minti sha biyar
  1. 1

    Zaki gyara kifinki, ki tabbatar kin cire kashin sosai, ki cire madaciyar ahankali karta fashe, zata lalata miki kifin,zaiyi daci.

  2. 2

    Sai ki wankeshi sosai da ruwa, sannan ki samu lemun tsaminki, ki yankashi,ki matse ruwan acikin ruwan wankin ki Kara wankewa domin karnin ya fita.

  3. 3

    Idan baki dashi kiyi using ruwan zafi da gishiri, kina sawa zakiga wannan santsin na jikinshi yana fita, sai ki wanke ki tsaneshi a abin a kwando.

  4. 4

    Sai ki wanke tarugunki,nasa tarugu zalla amma zaki iya using tattasai, ina son yajin ne, sai ki cire yayan cikin, sai ki jajjaga ki zuba atukunya, ki sa sinadarin dandano da ruwa Dan kadan, don ba,ason ruwa yayi yawa. Saboda idan yayi kauri yafi dadin sha romon.

  5. 5

    Sai ki yanka albasa ki zuba, kisa citta da dakakken kanumfari kadan.

  6. 6

    Sai ki samu pan ki zuba manja ki soya, da albasa sai ki zuba a ciki,sai ki daura a wuta kar kisa wuta sosai,sai ki barshi zuwa minti goma yana tausa, sai ki sauke, saboda shi idan ya dade a wuta zai narke, wajen daukowa zai rika rabewa.

  7. 7

    Zaki iya cinsa da bread da ruwan Lipton, Ana dangwalawa, ko kuma tuwon rogo, shima yana dadi sosai😋😋😋 ko ki hada da juice.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
rannar
Zaria City, I'm Married💞💞💞
kullum inason koyan abin da ban iya ba, kuma ina son gwadawa🍕🍤🍗🍜🍡🍝
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes