Steam semolina cake

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa 'daya
mutane uku
  1. Garin semolina qaramin Kofi biyu
  2. Kwai hu'du
  3. Mai kwatan karamar Kofi
  4. Sugar qaramar kofi daya
  5. Bakar Hoda qaramar cokali daya
  6. Kwatan cokali na gishiri
  7. Tukunyar turara abinci
  8. Ruwa
  9. Kofinturara abinci ko na gashin cake

Umarnin dafa abinci

awa 'daya
  1. 1

    Debo suga karamar Kofi daya, zuba a roba, fasa kwai hudu akan sugan.

  2. 2

    Bayan an fasa kwan sai a zuba gishiri kwatan qaramar cokali ciki, a debo Mai kwatan karamar Kofi a zuba ciki.

  3. 3

    A motsa hadin sosai har sai sikarin ta narke, idan Kuma anaso za a iya sakawa a blender Kamar yadda ake gani a hoton. Bayan sukari ta narke sai a kashe blender.

  4. 4

    A juye a roba idan a blender aka motsa shi. Idan Kuma a roba aka motsa shikenan. A debo garin semolina karamin Kofi biyu,

  5. 5

    A rinqa zubawa kadan kadan ana motsawa kamar na mintuna goma. Za a iya yi da mixer.

  6. 6

    Bayan an samu mintuna goma ana motsa shi, ga yadda zai Zama Kamar yadda aka gani a hoton. Sai a rufe shi ya samu Kamar mintuna goma a rufe.

  7. 7

    A nemo tukunyar turara abinci ko tukunya haka, A zuba ruwa a kasan tukunyar a saka marfin tukunya ko lariya a ciki Amma Kar ruwan ya wuce Rabin lariyar idan dashi za a yi.

  8. 8

    Idan da marfin tukunya kawai ne ma Kar ruwan ya haye marfin tukunyar.

  9. 9

    Bayan Nan sai a nemo kofin gashin cake ko dai duk wani irin Kofi da kike dashi ki shafe cikin da Mai,

  10. 10

    A bude cake din da aka rufen bayan minti goma,Idan an bude sai a dauko bakar Hoda qaramar cokali daya a zuba akai a Kara motsawa. Sai a daura tukunyar da za ayi turaran a daura a wuta.

  11. 11

    Bayan an Gama motsa bakar hodar a cikin cake din, sai a dauko kofin gashin cake ko na turaran, sai a zuba kullun a ciki, a jera a Kan marfin tukun

  12. 12

    Idan kina buqata sai ki Barbada ridi ko ko inibi ko cashew nuts a Kai, Ni ridi na Barbada a Saman na rufeshi bayan mintuna talatin na bude. A Nemi toothpick a Soma ciki, idan ya fito bakomai jiki to ya nuna, idan ya fito da tuwo tuwo to a barshi ya Dan qara dahuwa.

  13. 13

    Ga shinan bayan ya Gama turaruwa, na ciresu na juye a mazubi. Ga yadda cikin yayi.
    Yayi dadi sosai Kamar cake. Ana iya cinsa da shayi ko wani abin Sha.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
HAFSAT ABDULKAREEM
rannar
A food lover.❤️always ready to learn something new in zha kitchen 🍽️🍩😍
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes