Faten Tsakin Masara

Jamila Hassan Hazo
Jamila Hassan Hazo @Jermeelerh2

Akoda yaushe nalura ingari yayi sanyi Jama'ar gidana suna qaunar fate kowanne iri shiyasa namusu sabon samfuri

Faten Tsakin Masara

Akoda yaushe nalura ingari yayi sanyi Jama'ar gidana suna qaunar fate kowanne iri shiyasa namusu sabon samfuri

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 50mintuna
mutane 5 yawan
  1. Tsakin Masara wankekke
  2. 7Maggi
  3. Danyen citta
  4. Tafarnuwa
  5. Dafaffiyar wake kaďan
  6. Jajjagen tattasai da attarugu
  7. Tafashen Busashshen Rama
  8. Albasa me lawashi
  9. Yakuwa kaďan
  10. Dakakkiyar gyaďa 1tin

Umarnin dafa abinci

minti 50mintuna
  1. 1

    Ďaura ruwan zafi atukunya daidai misali kizuba jajjagen tattasai da attarugu da Danyen citta da tafarnuwa inya fara tafasa kijuye wankekken tsakin masara da dakakkiyar gyada atare da yakuwa sufara nuna

  2. 2

    Kikawo tafasashen Rama kijuye tareda albasa me lawashi kibarshi yanuna dakyau

  3. 3

    Kijuye dafaffiyar wake da maggi kimotsa saiki kashe wuta kibarta arufe na minti uku

  4. 4

    Aci dadi lfy 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Hassan Hazo
rannar
I Drive Pleasure While Cooking
Kara karantawa

Similar Recipes