Kayan aiki

  1. Aya
  2. Sugar
  3. Flavour
  4. ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki fara gyara ayar ki,ki fitar da duk wani datti da yake cikinta,sannan ki wanke ta sosai

  2. 2

    Bayan kin wanke zaki barta har sai ta bushe babu ruwa a jikinta

  3. 3

    Sannan zaki dora abinda zaki soya ayar a ciki,tukunya ko frying pan,sannan ki zuba ruwa daidai misali

  4. 4

    Idan ruwan ya tafasa sai ki kawo sugar da flavour ki zuba ki barshi ya dafu sosai,

  5. 5

    Sannan sai ki dauko ayarki ki zuba ki juya sosai,kina gama juyawa sai ki juye ta a kan faranti ki barta ta bushe zaki ga tayi fari shike nan."Alhamdulillah"

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Azeeyza
Azeeyza @Azeeyza13
rannar
Kano State,nigeria

sharhai (7)

Aisha M sani
Aisha M sani @cook_108444793
Assalamu alkm Yar uwa Yar aljannah ahalin yanxu aya nake me siga amma wllh taki bani hadin kai ruwa Yy yawa na barshi ya kone kuma suger din yay wani kauri Yy bris bris ya zanyi kuma wllh na sedawa ne

Similar Recipes