Kek mai chakulet (chocolate cake)

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

Ina godiya sosai ga Chef Suad da kokarinta wurin ganin ta koyar da mu wannan kek kuma mun koya. Hakika en gidanmu kowa ya ji dadinsa suna burin in sake yi musu irinshi. Na gode sosai

Kek mai chakulet (chocolate cake)

Ina godiya sosai ga Chef Suad da kokarinta wurin ganin ta koyar da mu wannan kek kuma mun koya. Hakika en gidanmu kowa ya ji dadinsa suna burin in sake yi musu irinshi. Na gode sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa kofi daya da rabi
  2. Suga kofi daya da rabi
  3. Garin cocoa rabin kofi da cokali babba biyu
  4. Firesh madara kofi daya
  5. Kwai manya guda biyu
  6. Rabin kofin ruwan zafi
  7. Bekin hoda cokalin shayi daya
  8. Bekin soda rabin cokalin shayi
  9. Gishiri 1/4 cokalin shayi
  10. Mai 1/4 kofi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayan yin kek din nan

  2. 2

    Ki zuba ruwan zafi a roba

  3. 3

    Sai ki zuba firesh madara a ciki

  4. 4

    Ki fasa kwai guda biyu a cikin wani kwanon daban

  5. 5

    Sai ki zuba mai ki karkada

  6. 6

    Ki zuba giishiri a ciki

  7. 7

    Sai ki koma cikin waccan madarar ki zuba bekin hoda, ki zuba bekin soda

  8. 8

    Ki zuba suga kofi daya da rabi din

  9. 9

    Sai ki tankade filawa a ciki. Ki tankade hodar cocoa itama a ciki. Idan kika saka haka nan zata duddunkule

  10. 10

    Ki juye hadin kwai da mai din a ciki

  11. 11

    Sai ki motsa. kwa6in zai yi ruwa kamar haka

  12. 12

    Sai ki saka a cikin abin da zaki yi gashi din

  13. 13

    Ki jera a cikin na'urar gashi ki gasa. Amma daga qasa zaki zuba ruwa a gwangwanin kek daban ki Saka a obin din tare da kek. Saboda ba zai bushe ba ko kwana nawa zai yi zai zauna da taushinsa. Haka Chef Suad ta koyar da mu kuma na karu sosai❤

  14. 14

    Idan ya yi minti talatin sai ki tsira abun sakace. Idan ya fito lafiya lau ya gasu. Idan kuma ya like bai gasu ba sai ki barshi ya qara kamar minti biyar sannan ki cire

  15. 15

    Toh na kammala🤗

  16. 16

    Kun ga yadda cikinsa ya yi nan

  17. 17

    Na kwaba whipping cream na yi ado a kai kuma ya yi dadi sosai

  18. 18

    ❤❤

  19. 19

    😘

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

Similar Recipes