Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kifi
  2. Alyahu
  3. Yakuwa
  4. Attargu
  5. Albasa
  6. Albasa mai lawashi
  7. Tomatir
  8. Kayan dandano
  9. Kanwa ko tokan miya
  10. Garin semovita
  11. Ruwa
  12. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki yanka alyahu ki wanke.ki yanka yakuwa ki wanke,sai albasa itama ki yanka ki wanke,ki yanka tomatir,ki jajjaga attargu,itama albasa mai lawashi ki yanka ki wanke ki ajiye gefe.shima kifi ki wanke shi sosai..amma nayi amfani da ice fish ne..

  2. 2

    Sai ki dauko tukunya sai ki fara zuba alyahu sai ki daura kifi a kai sai ki xuba tumatir ki saka albasa ki saka Attargu,sai mai lawashi sai ki xuba yakuwa sai maggi dai ki kara xuba alyahu ki saka tomatir sai ki kara jire kifi ki zuba mai lawashi ki xuba Attargu sai yakuwa sai sauran alyahu sai ki xuba maggi ki xuba mai sai ki dauko kanwa ki jika kadan sai ki zuba ruwa sai ki rufi..ki daura akan wuta baa motsawa..a haka har ya dahu..

  3. 3

    Tuwo sai ki daura a ruwan akan wuta indan ya tafasa sai kiyi talgi.ki zuba garin q cikin zuwa sai ki zuba a ruwan zafi indan yayi tafasa daya sai ki tuka ki xuba mai dan kadan..sai ki rufi ya silala sai ki zuba a lade..

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Shamsiya sani
Shamsiya sani @cook_16371942
rannar

Similar Recipes