Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki jika shinkafar cikin ruwan dumi yayi awa biyu masu kyau...shi zai baka rizalt mai kyau..bayan hakan Sai a wanke shinkafar asa ruwa akan wuta kamar kofin shan ruwa hudu..in ya tausa a zuba shinkafar a kara gishiri a juya a rife.
- 2
A wanke karas da green beans a yanka su yan madaidaita irin yankan cube a ajiye a gefe....Idan shinkafar ta dau hanyar dahuwa a zuba masa mai chokalin cin abinci hudu da sinadarin dandano biyu Sai a juya a rufe....a bashi minti goma,in ta dahu saura kamar minti biyar ta karasa Sai zuba masa kayan lambun nan a juyasu a hankali su hade Sai a rufe a rage wuta kasa har Sai ta dahu...
- 3
Miyar kuma zaki Daka kayan miyar ki, ki ajiye a gefe ki wanke kazar ki ki ajiye a gefe ki yanka albasa itama ki ajiye ta a gefe...sai ki sa tukunyar ki a wuta,in tayi zafi ki zuba mai,in man yayi zafi kisa albasa,dakakkiyar citta da tafarnuwa,ki juya su... su soyu na tsawon minti 1,Sai ki zuba kayan miyar ki soya ta minti 5-7...sannan ki zuba kazar nan ki zuba ruwa Kofi 1 & 1/2 ki sa kayan dandado da gishiri ki juya su hade Sai ki rufe ta..har Sai kazar nan yayi lugub.
- 4
Sai ki zuba curry dinki ki juya ki tsame naman ciki,ki dama filawa da madara in ba ta ruwa bace ki hada ta gari da filawa ki dama da ruwa chokali uku..Sai ki zuba,ki juya ta sosai Sai ki rufe ki rage wuta ki bata minti 5...in tayi maki kauri ki kara ruwa..Sai ki sauke ta...
- 5
Lallai zaki hadu dasu albasan nan da ya'ayan tarugu acikin miyar in kin lura...toh karki damu ki tace miyar da karamar kwando dukka Sai ki mayar tukunya ki daura kan wuta ki zuba kazar nan ki bata minti 3 kachal...zakiga tayi kyau tayi simut(smooth)
- 6
Sai dankali
Ki fere dankali ki wanke ta ki raba su gida 4 ko 6 ko wannen su..
Sai ki fere karas ki raba gida 4 a tsaye,ko wanne dayan ki yanka ta guda uku a karkace ta bada shape mai kyau..
Itama green beans a wanke a yanka ko wanne 4 a karkace kamar karas... - 7
Sai a hada su dukkan a tafasa kamar na tsawon minti 3..sai a zuba gishiri da dunkulen dandano a juya a rufe a bashi minti 2...sannan a juye a kwando ya tsane sosai sai a zuba masa mai a juya...
- 8
Sannan a kunna obin(oven)in yayi zafi,a zuba dankalin nan a farantin gashi a gasa ta tsawon minti 10-15...a dinga yi ana dubawa ana juyawa...in yayi har ciki sai a kashe wutar...an gama kenan
- 9
Yanayi
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Wanda aka rubuta daga
Similar Recipes

Dalgona coffee


Pita bread


Doughnut


Bread


Pancake


Cous cous da miyar dankali


Lemon mangwaro


Biskin shinkafar tuwo da miyar kayan lambu


Masa with vagetable soup


Fried rice


Chicken corn soup 2


Homemade ice cream


Farantin dankali


Dambun shinkafa


Meat pie


Shinkafa da nikakken nama


Cookies


Fried Rice


Pankasau Da Miyar Cabbage


Chicken corn soup


Fried rice mai kwakwa


Cookies 2


Nariyal(coconut)ladoo


Biskin shikafa


Dankali mai Curry


Sinasir


Fish casserole


Dafadukan shinkafa


Sinasir


Fanke

sharhai