Soyayyen naman sa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
Bauchi State

#NAMANSALLAH soyayyan naman sa da dadi sosai, barin ma in kasa a cikin abinci kana ci. Na gwada kuma yayi dadi sosai.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

Awa biyu
mutane hamsin
  1. Naman sa jinya biyu banda kashi
  2. Mangyada domin Suya
  3. Albasa manya guda goma
  4. Maggi guda hamsin
  5. Gishiri rabin ledar Mr chef
  6. Vedan rabin babban leda
  7. Citta Kofi biyu
  8. Curry ledar gino guda ashirin
  9. Dakakken Borkono Kofi biyu

Umarnin dafa abinci

Awa biyu
  1. 1

    Da farko na wanke hannuna sosai na yayyanka nama na. Gaskiya bana wanke naman layya, saboda ina aikin ne a guri tsaftacacce gurin da ba kuda. Bayan na yanka naman sai na cakuda naman da kayan hadi wato gishiri, maggi, vedan, curry, citta, borkono da albasa. Na bashshi yayi awa daya. A rufe.

  2. 2

    Sai na dora tukunyar tafashe na kara yayyanka albasa. Na rufe naman domin ya dahu. Awa daya na bashi domin ya dahu sosai.

  3. 3

    Anan ga naman har ya dahu na kwashe na xuba a roba.

  4. 4

    Sai na dora mangyada a wuta na yayyan ka albasa, bayan ta soyu.

  5. 5

    Sai na kwashe albasar na zuba naman nawa.

  6. 6

    Bayan ya soyu na kwashe gashi kamar haka.

  7. 7

    Aci dadi lpia!

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
rannar
Bauchi State
cooking is one of my best hobby
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes