Kayan aiki

  1. 2Markade ludayi
  2. Kabewa yanka 4
  3. Ganyen yakuwa
  4. Ganyen alayyahu
  5. Gyada danye rabin kofi
  6. 2Albasa babba
  7. Maggi dan gote na miyan taushe guda goma
  8. cokaliGishiri rabin babban
  9. 2Mai ludayi
  10. Qashin naman sa/ saniya
  11. Curry cokali daya
  12. Garin tafarnuwa rabin qaramin cokali
  13. 3Maggi guda
  14. cokaliGarin citta rabin

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke qashin man ki kisa a tukunya saiki hada dukkan kayan qamshin da na ambata a sama ki juye su kisa curry din kisa maggi 3 sai saka ruwa ba dayawa ba ki rufe naman ki ya tafasa sosai saiki xo ki juye ruwan tafasan ki saka mai ki soya naman ki tsame shi saiki zuba markaden ki akan mai ki soya sama sama saiki kawo ruwan tafashen naman ki juye.

  2. 2

    Daga nan Zaki gyara gyadan ki ki wanke ta saiki saka dan ruwa ki juye a blender ki markadeta ki juye a miyan ki, shima kabewa zaki markade ta ki juye.

  3. 3

    Saiki kawo dangote seasoning din ki da gishiri ki juye tare da qashin naman ki, zaki gyara ganyen yakuwa ki wanke shi ki juye shima.

  4. 4

    Sannan zaki rufe miyan ki zuwa minti 20 saiki gyara ganyen alayyahu ki wanke ki juye ki sauqe miyan ki kar alayyahun ya dahu shikenan.

  5. 5

    Zaki iya cin miyan ki da tuwo kala kala.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
rannar
Jigawa State Nigeria

sharhai

Similar Recipes