Kayan aiki

  1. Shinkafa yadda ake bukata
  2. Busashen kifi
  3. Crayfish dakakke
  4. 1Tomato paste sachet
  5. 1Pepper and onion paste sachet
  6. Albasa yankakkiya
  7. 2Bayleaf
  8. Jajjagen kayan miya
  9. Dandano
  10. Gishiri
  11. Kayan kanshi(curry,thyme,corriander,cumin)
  12. Ruwa
  13. Mai
  14. Ginger garlic paste

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki gyara kifin ki ki wanke ki aje gefe, sai ki dora tukunya ki zuba mai dai dai da yawan sanwarki.sai ki zuba albasa kadan ki zuba ginger garlic paste ki soya kadan.

  2. 2

    Idan ya dan soyu sai ki zuba tomato paste da onion and pepper paste ki barshi ya soyu sai ki kawo jajjagen kayan miyan ki ki zuba ki kara barin shi ya soyu.sai ki zuba bayleaf,dandano,gishiri da kayan kamshi ki juya sai ki tsaida ruwa dai dai yadda zai dafa miki shinkafar ki.sai ki zuba busashen kifi da crayfish ki rufe ya tafaso.idan ya tafasa sai ki zuba shinkafar ki rufe.

  3. 3

    Idan ta kusa nuna sai ki zuba sauran albasar ki kara ruwa ko dandano idan da bukata ki rage wutar ya karasa.Aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai (3)

Similar Recipes