Chicken shawarma

Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
Kano

Shawarma akwai dadi ga kuma sauki wajen yi ki gwada yar uwa da kanki zaki bani labari basaikin je kin siyo a restaurant ba zaki iya yin taki a gida kuma tayi dadi mai gida ma yayi santi.#SHAWARMA

Chicken shawarma

Masu dafa abinci 10 suna shirin yin wannan

Shawarma akwai dadi ga kuma sauki wajen yi ki gwada yar uwa da kanki zaki bani labari basaikin je kin siyo a restaurant ba zaki iya yin taki a gida kuma tayi dadi mai gida ma yayi santi.#SHAWARMA

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

4 yawan abinchi
  1. Filawa
  2. Yeast
  3. Baking powder
  4. Siga
  5. Gishiri
  6. Mai kadan
  7. Kayan cikin shawarma
  8. Kaza
  9. Cabeji
  10. Cucumber
  11. Karas
  12. Attaruhu
  13. Albasa
  14. Mai kadan
  15. Kayan magi
  16. Ketchup
  17. Bama ko salad cream

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki zuba filawarki a kwano saiki sa yeast,baking powder,gishiri kadan,siga ma kadan sai mai shima ba da yawa ba saiki cakuda,sai ki dakko ruwan dumi ki zuba shima kadan ki cakuda har sai yayi kamar kaurin doughnut saiki samu gurin dumi ki ajiye ya tashi.

  2. 2

    Sai hadin kayan ciki,da farko zaki wanke attaruhu da albasa ki yankasu kisa a tukunya kizuba ruwa kadan ki dura a wuta ya tafasa,saiki sauke ki dakko soyyayiyar kazarki ki yankata kanana kanana dogaye yanka ki zuba ta a cikin tafasashen attaruhu ki kara durawa ki zuba ruwa kadan shima idan ya fara tafasowa saikisa kayan magi da mai kadan aciki ki juya saiki rufeshi ruwan ya kama jikinshi saiki sauke.

  3. 3

    Saiki dakko cabejinki da cucumber da karas ki wankesu ki yankasu ma daidaitan yanka shikuma karas dn gogashi zaki yi saiki ajiye a gefe shima, saiki dakko kwabin ki ki kara bugashi sosai ki dakko abin murji kisa filawa akai ki yanko kwabin ki fadadashi saiki murza yayi cycle kada yayi tudu yayi falanfalan yadda idan ki ka dauka bazai yageba,dama kin dakko non stick kin shafa mai a jiki ki kunna wuta kadan saiki sa dough dinki da kika murza aciki ki gyara shi yadda bazai lankwasheba.

  4. 4

    Saiki rufe da murfi ya gasu zaki fara jin kanshi saiki bude ki juya daya barin shima ya gasu saiki kwashe kisa a leda kar ya sha iska haka zaki tayi har ki gama.idan kin gama saiki dakko bread dn guda daya ki shafa ketchup da salad cream ko bama kishafa ko ina yaji saiki dakko cabejinki dasu karas dinki ki zuba aciki amma ta tsaye ki dakko namanki da kika soya da attaruhu shima ki zuba saiki nannade kamar tabarmakisa tissue ko peper ki nade dashima sai aci haka zakiyi har ki gama.😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu ashraf kitchen
Ummu ashraf kitchen @cook_19629121
rannar
Kano
I luv cooking
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes