Kayan aiki

  1. Farar shinkafa
  2. Fulawa
  3. Yeast
  4. Egg (kwai)
  5. Ruwa
  6. Baking powder
  7. Sugar (suga)
  8. Salt (gishiri)
  9. Mai kadan

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tanadi farar shin kafarki ki jikata tayi awa shidda,
    Idan ta jika saiki stabtaceta ki tabbatar ta wanku sosai har saikin tabbata ba wani sauran datti aciki.

  2. 2

    Zaki kuma tanadi dafaffen shinkafa ko tuwo mai zafi,idan kin fitarda waccen jikakken shin kafar zaki hadasu wuri daya da dafaffenki,ki zuba fulawanki da yeast dinki duka acikin wancen dafaffen da kuma wanda kika jika.

  3. 3

    Saiki sakasu a blender kisa ruwa kadan ki fara Markadawa,da zaran ya fara nikuwa saiki zuba yeast dinki su ida nikuwa lokaci daya, koda zaki kare kullunki ya tashi insha Allah.saiki samu tsaftataccen mazubinki ki zuba kullun aciki kirufe kisashi awuri mai dan dumi na tsawonminti biyar zuwa goma.

  4. 4

    Sannan ki dauko hadiki da kika rufe kisa mishi baking powder da kwai,sugar da kuma gishiri kadan. Sannan ki daura kaskon ki na tuya a wuta yayi zafi,kisaka mai kadan saiki zuba kullunki acikin kaskonki da yake kan wuta,zaki iya rufewa na yan mintuna kadan, saiki bude kigani idan yayi saiki juiya. Idan kuma bakison wanda ake juiyawa zaki iya barinshi a bude.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen
rannar

Similar Recipes