Yar bagalaje (wainar rogo/ kosan rogo)

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Abincin karin kumallo me sauki. (Breakfast) Kusan kowa yana sonta. Tana da dadi sosai. D ftn za ku gwada don jin dadin ku.😂😀😃

Yar bagalaje (wainar rogo/ kosan rogo)

Abincin karin kumallo me sauki. (Breakfast) Kusan kowa yana sonta. Tana da dadi sosai. D ftn za ku gwada don jin dadin ku.😂😀😃

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mintuna
3 yawan abinchi
  1. Garin rogo gwangwani 3
  2. Jajjagen Attaruhu da albasa cokali 2
  3. yarkadan
  4. Magggi dan dandano 2
  5. Kayan kamshi
  6. Ruwan zafi daidai misali
  7. Man suya
  8. Tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

30mintuna
  1. 1

    Da farko za a zuba garin a roba a ciccire dattin da tsakuwar.

  2. 2

    Sai a kawo ruwan zafi a zuba akai har ya sha kan garin. A rufe yayi kamar mintuna 5.

  3. 3

    A zuba kayan hadin gaba daya a juya ya hade jikinsa

  4. 4

    Sai a dunga mulmulawa

  5. 5

    Sannan a fadada da hannu

  6. 6

    Sai a soya a cikin ruwan mai me zafi. Note: idan mai beyi zafi ba zata sha miki mai.

  7. 7

    A bari ta yi ruwan zuma shine ta soyu sai a juya a kwashe

  8. 8

    A ci da zafinta. Ni dai da kunun tsamiya nayi.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai (4)

Maryam Muhammad
Maryam Muhammad @Amira443
Kamar naji ta abakina 😍😋👌

Similar Recipes