Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki zuba nikakken namanki a tukunya ki zuba maggi da gishiri ki saka ruwa, saiki gyara albasa da attaruhu ki wanke ki yanka albasar kanana ki zuba acikin naman ki jajjaga attaruhun shima ki zuba a cikin naman saiki daura akan wuta.

  2. 2

    Saiki samu fulawar ki ki tankade ki zuba gishiri ki juya saiki zuba mai dai-dai gwargwado ki zuba ruwa ki kwaba har tayi miki dai-dai kamar kwabin meat pie saiki faffadata ki zuba mata farin mai ki rufe.

  3. 3

    Saiki koma gurin naman ki inya tsotse ki zuba mai kiyita juyawa harya samu amma ba soyuwa sosai ba sama-sama saiki kwashe.

  4. 4

    Saiki koma gurin fulawarki kina dauka kina murzawa kina ajiyewa harki gama.

  5. 5

    In kin gama murza fulawar ki sai kije ki daura kasko kan wuta in yayi zafi kina daura murzazziyar fulawar nan yadan gasu zakiga ta dago da kanta saiki dauke haka zakinayi harki gama.

  6. 6

    Saiki dawo ki debi fulawa kadan a kwano ki damata da ruwa saiki yanka fulawar dai-dai girman da kikeso kina mata ninkin dan kwali saiki zuba naman aciki ki shafa damammiyar fulawar ki domin kada ya bude haka zakiyi tayi harki gama.

  7. 7

    Saiki daura kaskon ki akan wuta ki zuba mai in yayi zafi ki saka samosan ki inya soyu ki juya shikenan kin gama samosa zaki iyaci da lemo ko shayi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

Similar Recipes