Awara da Kwai

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

Awara abinci mai dadi inason awara

Awara da Kwai

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Awara abinci mai dadi inason awara

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Waken suya
  2. Ruwan tsari
  3. Manja
  4. Kwai
  5. Man gyada
  6. Albasa
  7. Maggi
  8. Kishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke waken suyar ki ki cire duk wata kasa da datti saiki bayar a niko miki, ana niko miki saiki zuba manja saboda kumfar tayi kasa ki kara ruwa ki saka abin tatar koko ki tace, saiki daura tukunyar ki kan wuta ki juye ruwan waken suyar nan yayita dahuwa har saiya tafaso, yana tafasowa saiki debi ruwan tsarin ki a kofi ki yaryada zakiga awarar ta fara dunkulewa haka zakici gaba dayi har sai awarar ki ta gama hade jikin ta ainahin ruwan ciki ya zama fari tom awararki tayi.

  2. 2

    Saiki wanke abinda kika tace awarar ki juye awarar aciki ki daure sosai saiki danneta da abu mai nauyi koki rataye ta har ruwan jiki ya tsane.

  3. 3

    In ruwan ya tsane saiki yanka awarar ki dai-dai girman da kikeso ki jika maggi da gishiri ki zuba awarar a ciki tayi kamar minti biyar saiki cire.

  4. 4

    Saiki fasa kwanki a kwano ki yanka albasa ki zuba maggi rabi saiki daura farin mai a kasko in yayi zafi saiki kada kwanki kina daukar awarar ki kina juyawa cikin ruwan kwai kina sata a cikin mai a haka harki gama inta soyu ki juya daya barin inta soyu gaba daya ki kwashe anacin awara da yaji koda miyar da kikayi da dan attaruhu da albasa da kabeji aci dadi lfy.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes