Donut mai kwalliya

Mamu
Mamu @1981m
Lagos

Nayishine domin yara, yara sukanshigo mani ranar friday, kuma suna sonshi sosai.

Donut mai kwalliya

Nayishine domin yara, yara sukanshigo mani ranar friday, kuma suna sonshi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hr 30 minutes
10yawan abinchi
  1. 3Fulawa kofi
  2. 1/4siga
  3. 1 tspgishiri
  4. 2 tspyeast
  5. 1/4kofi bota
  6. 1kwai
  7. 1/2kofi madara
  8. 1 tspvanilla
  9. 2-4 tbspruwa
  10. Kayan kwalliyan saman donut
  11. 1/4Cocoa powder
  12. Icing sugar 3 kofi
  13. Colour: pink
  14. 1 cupMadara
  15. Sprinkle
  16. Flavour

Umarnin dafa abinci

1hr 30 minutes
  1. 1

    Nakawo fulawa da suga nahada wuri daya, nasamu wata roba nakawo warm madarata na dauko yeast na juye aciki nabarshi a rife na dan lokaci, nafasa kwai najuye acikin ruwan yeast din, da vanilla flavour na,sannan na hadasu wuri daya nakawo ruwa nasa, na cakude, har suka fara hadewa, na kwashe dough din nakaishi inda zanyi aiki akanshi, nakawo bota nasa, natabbatar daya shiga ko ina, sannan nayita murza har komi yahade, nayi murza kusan minti 40.

  2. 2

    Da yayi taushi sosai saina kawo roba nasashi waje mai dumi na minti 30, ina budewa ya kumburo sosai, saina kara murzawa, sannan nasa cutter nafidda shape din, sannan na dora mai a wuta, amma ba'ason man yayi zafi sosai daidai, nakawo donut din ina soyawa, da yayi saina kwashe.

  3. 3

    Nazuba icing sugar a mixer nakawo madara nasa aciki, da flavour nakawo ruwa kadan nayi mixing nasu har sukayi smooth sannan naraba biyu daya nasa pink colour aciki, dayan kuma na barshi a farinshi

  4. 4

    Nakara xuba icing sugar a mixer, nakawo cocoa powder da madara da flavour shima nayi mixing nashi, sannan narabashi biyu, nakarasa cocoa powder aciki don yayi duhu sosai, sannan na dauko donut dina ina sakawa aciki, dana gama nasama wasu sprinkles akai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mamu
Mamu @1981m
rannar
Lagos
Eating is necessity but cooking is an Art, i just love cooking
Kara karantawa

sharhai (4)

Similar Recipes