#tuwonshinkafacontest.. Tuwon shinkafa miyar zogale

Deejarh berver
Deejarh berver @cook_12476657

Babu kamar tuwo abinci ne mai kara lafiya ga kuma dadi ga saukin yi, indai kika dage kika kokarta zaki iya tuwo kalakala ke dai kikasance mai gwada abunda kika koya shi tuwo akan ci shi da miya akan cishi gaya kokuma ayi kwadansa.

#tuwonshinkafacontest.. Tuwon shinkafa miyar zogale

Babu kamar tuwo abinci ne mai kara lafiya ga kuma dadi ga saukin yi, indai kika dage kika kokarta zaki iya tuwo kalakala ke dai kikasance mai gwada abunda kika koya shi tuwo akan ci shi da miya akan cishi gaya kokuma ayi kwadansa.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Farar shinkafa
  2. Ruwa
  3. Ledar kullawa

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki wanke farar shinkafarki sai ki dora ruwa ki zubata aciki kirufe yayita dahuwa idan shinkafar ta dahu saiki samu muciya ki tukashi sosai da sosai har sai yayi laushi yayi danko ya hade jikinsa sai kisamu leda kina sakawa kina kina daure ledar sai aci lafiya da miyar da akeso

  2. 2

    Yadda zaki hada miyar zogale da danyar gyada Dafarko zaki samu zogalenki bushashe sai ki samu ruwa mai kyau ki zuba sa aciki kibarshi, sai ki jajjaga attaruhu da daddawa ‘yar k’adan da kuma tafarnuwa da koren

  3. 3

    Tattasai da danyar gadarki sai ki dakasu, sai ki yanka albasarki mai dan yaea sai ki zubata acikin tukunya ki zuba mai kisaka markadadden kayan miyar ki cokali 4

  4. 4

    Sai ki ta siyawa har sai miyar tafara soyuwa sai ki zuba curry kita juyawa sai ki zuba wannan abubuwan dakika daka sai ki jujjuya su ki zuba ruwa rabin kofi ki zuba kifin ki

  5. 5

    Ko nama ni da kifi nayi sai kibarshi yatafaso sai ki matse zogalenki ki zuba aciki kisa maggin

  6. 6

    Ki ki jujjuya sannan sai ki rufe ki rage wutar idan yayi kamar mintuna 7 haka zai ki jujjuya kikara barinsa yayi minti 2 sai ki sauke kici da kowacce irin tuwo

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Deejarh berver
Deejarh berver @cook_12476657
on

Comments

Similar Recipes