Share

Ingredients

  1. Shinkafan tuwo
  2. Ruwa
  3. Tukunya
  4. Zogale danye
  5. Markadaddiyar gyada
  6. Albasa
  7. Mai
  8. Seasonings
  9. Spices
  10. Tumatir
  11. Tattasai
  12. Attaruhu

Cooking Instructions

  1. 1

    Ki jika shinkafa tun safe da yamma ki dora ruwa a tukunya ki wanke shinkafan ki.zuba ki rufe amma ba ruf ba

  2. 2

    Idan ya zama saura kadan ruwan sai ki dauko muciya ki tuka tuwonki ta ko ina ya tuku sai ki rage wuta ki rufe

  3. 3

    After 10 to 15minutes yayi.sai ki sake tukawa sai ki kisa a leda ki kulle kamar haka

  4. 4

    Ki gyara kayan miyanki ki jajjaga ko ki markada ko ki yanks

  5. 5

    Ki zuba manja a tukunya idan yayi zafi ki zuba yankakkiyar albasa da yawa idan tafara soyuwa ki zuba kayan miyan ki har su soyu amma ba sosai ba

  6. 6

    Sai ki zuba ruwa ki dama gyadan ki zuba aka ki rage wuta har gyadan ta nuna

  7. 7

    Sai kisa zogale kisa spices da seasonings ki gauraya ki rufe

  8. 8

    Ki bashi kamar 15 to 20minutes yayi shikenan

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Ghalee Tk Cuisine
Mrs Ghalee Tk Cuisine @cook_13808718
on
Jos

Comments

Similar Recipes