Share

Ingredients

30mins
  1. Gyada
  2. Gasara
  3. Lemon tsami
  4. Sugar
  5. Madara da kwakwa idan kina bukata
  6. Dafaffiyar shinkafa

Cooking Instructions

30mins
  1. 1

    Da farko zaki zuba gyadar ki a akaramin bowl ko roba saiki dama ta sosai.

  2. 2

    Saiki sami rariya ta tace ruwa ko normal rariya ki tace gyadar acikin tukunyar da zaki dafa gyadar taki.

  3. 3

    Saiki dora tukunyarki akan stove ki kunna wuta saiki zuba wannan dafaffiyar shinkafar taki ko kwakwa da kika gurza acikin ruwan gyadar ki rufe tukunyar.

  4. 4

    Idan ruwan gyadar ki ya fara zafi saiki zo ki tsaya akan sa saboda karta tafaso ta zube idan kuma ta zube maikon gyadar taki ne ya zube, kita juyawa dan ki hanata zubewa kuma tana tafasa gafin gyadar yana fita.

  5. 5

    Idan ta gama tafasar ta sosai gafin gyadar ya fita zaki ga tayi kasa ta daina kumfa saiki zuba gasarar ki a babban abu ki juye ruwan gyadar akai.

  6. 6

    Sai ki maza ki fara juyawa dan kar tayi miki gudaji amma kuma bada karfi ba ahankali saboda karya tsinke.

  7. 7

    Saiki zuba lemon tsami me hade da yar gasara acikin kunun naki zaki ga ya kara kyau, bayan wasu yan mintuna saiki zuba madara aciki ki juya shikenan.

  8. 8

    Kunun gyada ya hadu ga kuma kosai😋😋😋

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummukulsum Mustapha Ahmad
on
Kano State

Comments

Similar Recipes