Share

Ingredients

  1. Kayan miya(Attaruhu, Albasa,timatir,tattasai)
  2. Gyada(Dakakkiya)
  3. Manja/man gyada
  4. Alaiyahu
  5. Lawashin albasa
  6. Yakuwa
  7. Nama/tantakwashi/kaza
  8. Kayan dandano

Cooking Instructions

  1. 1

    Ki wanke nama/tantakwashi/kaza ki tafasa da salt da kayan kamshi.A tsame a ajiye

  2. 2

    A zuba markaden kayan miya a tukunya a tafasa a soya da mai da kayan dandano sai a zuba ruwan tafashen nama nan.

  3. 3

    A feraye kabewa a wanke a yanka a zuba a cikin miyar nan a dafa suyi laushi sai a tsame a daka ko a markada a blander, a mayar a zuba cikin miyar.A saka naman nan da aka tafasa.

  4. 4

    A daka gyada a zuba a miyar a rage wuta dan ta dahu.

  5. 5

    A yanka lawashi a wanke a zuba a cikin miyar.

  6. 6

    A yanka yakuwa a wanke itama a zuba a miyar.

  7. 7

    Daga karshe idan komai yayi,gyada tayi laushi lawashin albasa da yakuwa sun hadu sai a zuba maggi da aliyahu,a bashi minti kadan sai a sauke.

  8. 8

    Miyar taushe ta hadu.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jahun's Delicacies
on
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Read more

Similar Recipes