Ferfesun kifi

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yana cikin daya daga cikin da nafoso sosai Kuma hakama iyalaina

Ferfesun kifi

Yana cikin daya daga cikin da nafoso sosai Kuma hakama iyalaina

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kifi
  2. Mai
  3. Attarugu
  4. Yumatur guda daya
  5. Albasa
  6. Maggi dasauran sinadaran da kikeso
  7. Cinnamon powder dan kadan
  8. tafarnuwaCitta da
  9. Curry da thyme
  10. Tumeric

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke kifinki da ruwan zafi kitabbata dattin duk yafita sai kizuba a kwana mai safta ki ajiye a gefe

  2. 2

    Sai kidauko tukunyar da zakidafa da ita kizuba ruwa dan daidai sannan kidaura a wuta sai kiyanka albasa kizuba aciki ki jajjaga attarugu da tumatur kwaya daya kixuba aciki

  3. 3

    Sannan kizuba Maggi dasauran sinadaranki sannan Kuma kizuba cinnamon dinki kisa tumeric da curry da thyme sai kibarta tatafasa sosai sannan kisa mai Dan kadan sai kixuba kifin akai sannan kidan diba ruwan miyan kizuba akai amma kada kijuya don kifin kar ta farfashe

  4. 4

    Sannan kirufeta nadan lokaci kadan idan yadahu sai kisauke. Zaki iya cinta haka kokuma kihada da duk irin abincin da kikeso

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai (8)

Maman jaafar(khairan)
Maman jaafar(khairan) @jaafar
Masha Allah delicious 😋😋😋😋

Similar Recipes