Awara

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Nida iyalaina munkasance munason cin awara amma kuma bantaba gwadawaba sai wannan karon kuma alhmdllh nayishi yanda yakamata kuma munci munmore

Awara

Nida iyalaina munkasance munason cin awara amma kuma bantaba gwadawaba sai wannan karon kuma alhmdllh nayishi yanda yakamata kuma munci munmore

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Waken suya
  2. Ruwan tsami
  3. Manja
  4. Hadin souce
  5. Albasa
  6. Attarugu
  7. Tafarnuwa
  8. Citta
  9. Mai
  10. Maggi DA saurna sinadaran da kikeso
  11. Curry DA tumeric

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara waken kicire dattin duka tazama fes sannan kiwanketa sai kijika nadan wani lkci sannan kikai amarkada miki sai kizo kizuba manja akai kikara ruwa kadan sai kitace da abun tatan kamu

  2. 2

    Bayan kintace sai kisamo tukunya mai dan fadi kixuba aciki sannan kidaura a wuta kibari yataso kamar zaizube sannan kidauka ruwan tsamin kizuba akai zakiga yakoma baya yafara hada kanshi

  3. 3

    Sai kibarta tagama haduwa sannan kijuye a bunch tatan kamun kimatseshi sosai kidaure kibari ruwan yagama fita tas sannan ki yanka sai kisoya

  4. 4

    Bayan kinsoya sai ki ajiye agefe sannan kiyanka albasa kijajjaga attarugu da tafrnuwa tareda citta sannan kidaura tukunya awuta kisa mai kadan idan tayi zafi sai kizuba albasa da citta da tafarnuwa kisoyata bayan kinsoya sai kizuba attarugu kisa ruwa kadan sannan kizuba maggi da sauran sinadaran sannan kizuba curry da tumeric kijujjya sannan kidauko awaran kijuye akai DWI kijujjuya komai tahade sannan kidan barta nadan mintuna kadan sai kisauke

  5. 5

    Idan kuma bakyason souce zaki iya cinta da yaji kokuma ita kadai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes