Gashassen hakarkarin rago

leemerhhskitchen
leemerhhskitchen @cook_14199480
Adamawa state

#namansallah wannan salon girki nada dadi sosai. Farko dana fara yinshi ina gamawa aka chinye a Kitchen. Shi nayi a sallah kuma duk wanda suka chi sunche ya musu dadi

Gashassen hakarkarin rago

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#namansallah wannan salon girki nada dadi sosai. Farko dana fara yinshi ina gamawa aka chinye a Kitchen. Shi nayi a sallah kuma duk wanda suka chi sunche ya musu dadi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Hour 2mintuna
5 yawan abinchi
  1. Rabin kilo hakarkarin rago
  2. Karamin chokali barkono baki
  3. Karamin chokali garin chitta
  4. Karamin chokali curry
  5. 2Maggi guda
  6. Babban chokali attarugu
  7. Chokali Karami dakakken tafarnuwa
  8. Karamin chokali garin coriander
  9. Rabin ruwan lemun tsami
  10. 2Mai geda babban chokali
  11. 1Soy sauce babban chokali
  12. 1Tumatur na kwalba babban chokali
  13. Ruwa rabin kofi

Umarnin dafa abinci

Hour 2mintuna
  1. 1

    Ki wanke hakarkarin ki saka a kwano. Ki zuba barkono baki da garin chitta

  2. 2

    Ki zuba curry da maggi. Ki zuba attarugu

  3. 3

    Ki zuba dakakken tafarnuwa da ruwan lemun tsami da garin coriander

  4. 4

    Ki zuba mai geda ki motsa shi da kyau. Ki saka a fridge na hour 2 ko ki barshi ya kwana. Domin hadin ya shiga chiki

  5. 5

    Ki shafa butter a kan pan saiki jera hakarkarin a kai. Ki gasa na minti 45

  6. 6

    Bayan yayi ki chire shi a wuta

  7. 7

    A wani tukunya ki zuba soy sauce da tumatur na kwalba da garin coriander. Ki saka wuta kadan

  8. 8

    Ki zuba ruwa a chikin kwanon da kikayi hadi ki juye a tukunya

  9. 9

    Ki saka hakarkarin ki motsa da kyau. Ki barshi ya nuna na minti 3

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
leemerhhskitchen
leemerhhskitchen @cook_14199480
rannar
Adamawa state
Catering service 🎂🍪🍛Cooking classesBaking classesMore information 08142922888IG: leemerhhs_kitchen
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes