Shawarma

fauxer
fauxer @fauxer
kebbi State

#shawarma.Inason shawarma sosai ni da iyalina.Nakan masu bazata da wannan a duk lokacin da nakeson sasu nishadi da farinciki.Shawarma abinci ne sosai da nakeso domin yana dauke da sinadarai na kayan ganye wanda ke gyara fata tare da bamu kariya daga cututtuka da izinin Allah,cucumber ta na narkar da kitsen da ke jikin dan adamg,karas na bada kariya da cutar daji(ulcer),yana kuma taimakawa gurin rage ciwon zuciya da mutuwar jiki.Kabeji yana rage kumburi,kyaikayi da kuma hawan jini a kuma sinadarin protein wato nama a ciki.Nakan ci lokacin da bana bukatar wani abu mai nauyi a ciki.

Shawarma

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

#shawarma.Inason shawarma sosai ni da iyalina.Nakan masu bazata da wannan a duk lokacin da nakeson sasu nishadi da farinciki.Shawarma abinci ne sosai da nakeso domin yana dauke da sinadarai na kayan ganye wanda ke gyara fata tare da bamu kariya daga cututtuka da izinin Allah,cucumber ta na narkar da kitsen da ke jikin dan adamg,karas na bada kariya da cutar daji(ulcer),yana kuma taimakawa gurin rage ciwon zuciya da mutuwar jiki.Kabeji yana rage kumburi,kyaikayi da kuma hawan jini a kuma sinadarin protein wato nama a ciki.Nakan ci lokacin da bana bukatar wani abu mai nauyi a ciki.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa biyu
  1. Domin kwabin biredin shawarma ana bukatar:
  2. kofi uku da rabi na fulawa
  3. Karamin cokali biyu na bakar hoda
  4. da rabi na yeast Cokali 1
  5. na madarar gari Cokali 2
  6. na sikari Cokali 2
  7. Rabin cokali na gishiri
  8. na mai Cokali 2
  9. Ruwa daidai da yadda zaya kwaba hadin ya game jikinsa
  10. Domin hada abubuwan da ke cikin biredin shawarma ana bukatar:
  11. Nama wanda aka yanka sirara a tsaye
  12. na curry Cokali 2
  13. na thyme Cokali 1
  14. Dunkulen maggi biyu
  15. na masoro Cokali 1
  16. Rabin cokali na citta
  17. guda uku manya da aka jajjaga Tafarnuwa
  18. Garin yaji cokali daya
  19. Attarugu biyu jajjagagge
  20. na mai Cokali 4
  21. Kofi daya da rabi na yankakken kabeji
  22. Karas guda uku da aka gurza
  23. Cucumber biyu da aka yanke tsaye sirara
  24. Kofi daya na mayyoinse
  25. Rabin kofi na Ketchup
  26. Kofi daya na yankakken latas
  27. Rabin kofi na tumatur da aka yanke tsaye

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Yadda ake hada biredin shawarma:Zaki sa ruwa kadan mai dumi a kofi kisa yeast ki motsa ki barshi tsawon minti biyar.Idan kikaga kumfa alamar yeast in na da kyau kenan.

  2. 2

    Sai ki hada kayanki busasshe na hadin kwabin kisa cokali daya na mai.

  3. 3

    Ki zuba yeast a ciki bayan kin motsa.

  4. 4

    Sai ki kwaba har ya hade jikinsa.Ki murza sosai tsawon minti goma.Hakan zayasa biredinki yayi taushi.

  5. 5

    Sai asa a leda a rufe tsawon awa daya abarshi ya tashi.Wannan bayan ya tashi kenan.Yaninka girmansa sau biyu.

  6. 6

    Acire iskan da ke ciki ta amfani da danna kwabin da hannu.

  7. 7

    A raba shi kashi goma na kwallaye.

  8. 8

    Sai a barsu a rufe tsawon minti goma.

  9. 9

    A dauki ball daya.A fadada da hannu.

  10. 10

    Sai a murzata da fadi ta fito gewaye.

  11. 11

    A shafa mai da fulawa a sama domin kada idan an dora daya a sama ya like.Ayiwa sauran kwallayen tara kamar yada akayiwa ta farko.

  12. 12

    A dora kasko a shafa mai ajikin a gasa biredin kowane gefe.Kada acika wuta.Idan yayi sai a sauke.A rufe.

  13. 13

    Hada shawarma:Za a hada rabin cokalin na mosoro,citta,attarugu,tafarnuwa,maggi,mai,curry, thyme da ketchup a cikin naman a gauraya.A barshi tsawon away daya.

  14. 14

    Sai a dora kasko a wuta a dafa naman.Har ya tsotse ruwan jikinsa kayan hadin ya hade jikinsa.

  15. 15

    A hada mayyyonaise da ketchup a sa sauran rabin cokalin mosoro a motse.

  16. 16

    A hada yankakkun kayan ganye guri daya asa hadin mayyonaise da ketchup a ciki a motsa.

  17. 17

    Sai a dauko biredin,a shafa masa hadin mayonnaise da ketchup a tsakiya.

  18. 18

    Sai a zuba hadin kayan ganye mai mayonnaise a ciki,sai nama,tumatur,kabeji da aka rage sai gurzajjen karas. Sai a zuba hadin mayonnaise a sama.

  19. 19

    Sai a nade kamar tabarma.

  20. 20

    Zaki iya sa takardar foil ko tissue ki ninke saboda kar ya bata jiki gurin ci.

  21. 21

    Idan aka tashi ci za a iya dumamawa.Ana iya hada shi da dankali gurin ci ko aci shikadai.Ayi girki cikin nishadi da farinciki.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
fauxer
fauxer @fauxer
rannar
kebbi State
many listen to music when depressed . When in such situation i go to my kitchen. Cooking is the only thing that can never get me exhausted and makes me forget my worries
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes