Shawarma

Rahinerth Sheshe's Cuisine
Rahinerth Sheshe's Cuisine @cook_17350184
Kano @Danladi Nasidi Housing Estate.

#SHAWARMA
Shawarma na daya daga cikin abinda nakeso kuma nafison in yita da kaina ta fiyimin dadi.

Shawarma

#SHAWARMA
Shawarma na daya daga cikin abinda nakeso kuma nafison in yita da kaina ta fiyimin dadi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Hadin biredin
  2. Flour Kofi uku
  3. Yeast cokali daya
  4. Gishiri kadan
  5. Man gyada
  6. Sugar kadan
  7. Hadin naman
  8. Nama
  9. Dandano
  10. Gishiri
  11. Kayan kamshi
  12. Chicken spice
  13. tafarnuwaSauce din
  14. Mai
  15. Attaruhu
  16. Kayan hadin mayonnaise din gida
  17. Kwai guda daya
  18. Gishiri kadan
  19. Sugar rabin cokalin shayi
  20. Vinegar cokali daya
  21. Vegetable oil Kofi daya
  22. Hadin ketchup
  23. Tumatir manya
  24. Sugar
  25. Gishiri
  26. Vinegar
  27. Kayan cikin shawarmar
  28. Kabeji
  29. Karas
  30. Cucumber
  31. Koren tattasai
  32. Kayan hada sauce din tafarnuwa
  33. Tafarnuwarabin kofi
  34. Vegetable oil Kofi daya
  35. Lemon tsami guda daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Hadin mayonnaise: Za'a samu blender (in anada hand blender tafi yi). A fasa kwai a zuba, sai a zuba gishiri, sugar, vinegar,(In babu za'a iya sa lemon tsami)

  2. 2

    Sai a markada, sai ana zuba man ana markadawa har yayi kauri

  3. 3

    Sai kuma hadin ketchup: Zaa samu tumatir manya masu kyau a wanke, sai a zuba a tukunya a dafashi, inya dahu zaaga fatar ta fara salubewa daga jikinsa, sai a sauke abarshi ya huce inya huce sai a zuba a blender asa ruwa a markadashi, inya markadu sai a tace shi abar iya ruwan da aka tace, a samu pan a zuba a ciki asa gishiri, vinegar, sugar a tona abarshi ruwan ya kafe zaa ga yayi kauri shikenan sai a sauke a barshi yayi sanyi.

  4. 4

    Zaa zuba flour, gishiri, mai, yeast sai a kwaba shi a rufe shi abarshi ya tashi

  5. 5

    Sai a rarrabashi, a murzashi yayi fadi kamar haka

  6. 6

    Sai a dora kasko a wuta mara kamu In yayi zafi sai a dauko asa, in bayan yayi sai a juya daya barin Haka za'ayita yi har a gama.

  7. 7

    Hadin Nama: Za'a samu nama zallar tsoka a yankashi a tsaye a wanke, sai a zuba masa dandano, gishiri, kayan kamshi, chicken spice, tafarnuwa da albasa sai a tona, sai abarshi ya hade jikinsa na tsahon awa daya ko fiye da haka

  8. 8

    Sai a daukoshi a zuba a kasko ayita tonawa har ruwan jiki ya tsotse, sai a jajjaga attaruhu a zuba asa mai kadan a rage wutar abarshi ya karasa.

  9. 9

    Sai a wanke su kabeji a yankasu, a hada mayonnaise da ketchup da sauce din tafarnuwa a tona sai a dauko biredin shawarmar a shafeshi dashi sai a zuba su kabeji a zuba naman a nade shawarmar shikenan angama.

  10. 10

    Yadda ake sauce din tafarnuwa: Za'a samu tafarnuwa mai kyau a gyarata a zuba a abin nika (blender) a zuba mai asa lemon tsami a markada har saita niku sai a samu mazubi a juye shikenan ana amfani da ita a shawarma ko duk abinda ya danganci harkar gashi.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Rahinerth Sheshe's Cuisine
rannar
Kano @Danladi Nasidi Housing Estate.
Tun ina yarinya na taso da kaunar girki da sarrafa Shi kuma mahaifiya ta tabani goyon baya ta hanyar koyamin
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes