Markaden kankana da gwanda

Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
sallari qts Kano

Yana matukar kara lpy da gyara jiki,idan za’a sha wannan kullum sau daya a rana,za’aga amfanin shi😜dadi kam kuma dama ba’a magana 😋

Markaden kankana da gwanda

Masu dafa abinci 8 suna shirin yin wannan

Yana matukar kara lpy da gyara jiki,idan za’a sha wannan kullum sau daya a rana,za’aga amfanin shi😜dadi kam kuma dama ba’a magana 😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Gwanda
  2. Kankana
  3. Madarar gari ko ta ruwa
  4. Siga
  5. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Wannan sune abun da muke bukata,gashi nan na yanka gwanda ta kanana,ga sugar chokali daya saboda bana son zaqi,amma zaa iya karawa yafi haka,se kuma madarar gari gata nan na kwaba da ruwa.

  2. 2

    Gashi nan kamar yadda kuka nayi a vedion kasa👇🏻na zuba siga d madara a cikin gwanda,yanzu zan markada har se yayi laushi sosai,shikenn na gama markaden gwanda ta

  3. 3

    Itama kankana gata nan kamar yadda naiwa gwanda na zuba madara da siga a ciki na markada yayi laushi sosai

  4. 4

    Se a kawo kofi a zuba gwanda rabi sannan itama kankana a zuba rabi kamar nayi a vedion kasa👇🏻shikenn markaden ki ya kammala,ni kam a wajen ma nake shanye nawa😜idan anaso kuma zaa sashi a na’urar sanyi domin ya yayi sanyi se a sha.

  5. 5

    Karin bayani:zaa iya dama madara da ruwa me sanyi idan anaso,amma ni banason sanyi da yawa dan haka nayi amfani da ruwa mara sanyi,domin sanyi yana da matukar illa a jiki,a kiyaye

  6. 6

    Da fatan za’a gwada

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
rannar
sallari qts Kano

sharhai

Similar Recipes