Tuwon dawa

Z.A.A Treats
Z.A.A Treats @mamanNurayn
Sokoto

#GWSANTYJAMI❤️ Wannan tuwon gargajia ne mai matuwar Dadi da anfani a jiki

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. Garin dawa
  2. Kanwa
  3. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko Zaki tanadi kayan girkin ki kamar haka

  2. 2

    Sai ki daura ruwa akan wuta har sai sun tafasa

  3. 3

    Sannan sai ki raba garin dawarki gida biyu ki aje dayan a gefe dayan Kuma ki kwaba shi da Dan kauri amma ba sosai ba,idan ruwanki sun tafasa sai ki dauko wannan kwabin ki zuba shi a tafasashen ruwanki kisa miciya kina juyawa

  4. 4

    Idan kin zuba sai ki dauko kanwa da kika jika ki zuba a cikin talgen ki.sai ki rufe tukunyar ki bari ta sulala

  5. 5

    Bayan ta sulala sai ki dauko garin dawar da kika aje kina zubawa kadan kina tukawa har sai ya tuku sosai Kuma kaurin shi yayi daidai.

  6. 6

    Idan kin gama tuka tuwon sai ki rufe tukunyar har ya dahu sosai sannan sai ki sauke ki zuba a muzubi.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

Wanda aka rubuta daga

Z.A.A Treats
Z.A.A Treats @mamanNurayn
rannar
Sokoto
I love cooking.
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes