Tuwon dawa

ummusabeer
ummusabeer @cook_12539941
Kano

#WAZOBIA Abincin gargajiya ne mai dadi ga kara lafiya a jiki.

Tuwon dawa

#WAZOBIA Abincin gargajiya ne mai dadi ga kara lafiya a jiki.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 3Garin dawa kofi
  2. Kanwa ungurnu kadan
  3. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaa hada kayan kamar haka

  2. 2

    A zuba ruwa cikin tukunya a dora kan wuta a barshi ya tafasa, sai a jika wannan kanwar sannan a juye cikin tafasasshen ruwan, zaa ga ya dan canja kala kadan sannan sai a debi garin kamar kofi daya a dama da ruwan sanyi sai a juye cikin ruwan tukunyar.

  3. 3

    Sannan a juya da abin juyawa

  4. 4

    Sai a barshi ya dahu sosai na tsahon minti 20,zaa ga yana yauki idan ana juyashi sai a sauke daga kan wutar.

  5. 5

    A zuba sauran garin a tuka sosai.

  6. 6
  7. 7
  8. 8

    Idan ya tuku zaa ga ba gudaji a cikin sa

  9. 9

    Sai a cire muciyar a yi amfani da mara wajan hade shi sannan a zuba ruwan zafi tafasasshe

  10. 10

    Sannan a mai dashi kan wuta a barshi ya dahu na tsahon minti 30,sannan kuma a rage wuta sosai dan kar ya kama

  11. 11

    Sannan a sauke a tuka, sannan a kwashe a zuba cikin mazubi.

  12. 12

    Shikenan tuwo ya hadu, zai kuma fi dadi da miyar yauki kamar kubewa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
ummusabeer
ummusabeer @cook_12539941
rannar
Kano
Cooking is my pride
Kara karantawa

Similar Recipes