Pankasau Da Miyar Cabbage

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Wannan pankasau a level ne ba filawa ba hade hade irin na gargajiya me dadin nan #method
#pankasau #frying

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

2hours
7 yawan abinchi
  1. 5Garin alkama kofi
  2. Yeast chokali babba 1
  3. Sugar chokali babba 1
  4. 1Albasa babba
  5. Gishiri kadan
  6. Mai kwalba 1 na suya
  7. Miyar cabbage
  8. 1Cabbage
  9. 10Karas
  10. 1Green peas kofi
  11. 1Mai chokalin miya
  12. 2Nikakkaun kayan miya chokalin miya
  13. 4Dandano
  14. Curry
  15. Thyme
  16. Mixed spice

Umarnin dafa abinci

2hours
  1. 1

    Ki surfe alkama ki wanke ki shanya kada ki bari tasha ruwa wasu basu wankewa surfewa kawai suke su hece amma ni na wanke

  2. 2

    Ki zuba kofi 5 na filawa cikin bucket ko roba ki zuba yeast da sugar ki kwaba da kauri

  3. 3

    Idan ya tashi ki buga sosai sannan ki aza mai bisa wuta yayi zafi ki yanka albasa ki zuba

  4. 4

    Kisamu roba me zurfi ko kwarya ki shafe ta da mai daga waje sannan ki wanke hannin ki da ruwa ki debo kadan ki zuba bayan robar

  5. 5

    Sannan ki dan huda saman 2 ko 3 ko ma daya sanna ki juya ki sa ciki mai me zafi ki soya duka gefen 2

  6. 6

    Idan ya soyu zakiga ya fara ja daga gefe se kinayi kina juyawa har yayi

  7. 7

    Idan kin kwashe ki dan soya albasa kisa asama don karin dadi

  8. 8

    Ita miyar ba abuce me wuya ba
    Zaki zuba mai yayi zafi ki zuba kayan miya su soyu sannan ki zuba ruwa

  9. 9

    Ruwan na bisa kisa naman kisa dandano curry thyme ka kayan kamshi da green peas ki rufe

  10. 10

    Idan naman ya dahu se ki zuba cabbage da karas sudan sulala shikenan miya ta hadu

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes