Kayan aiki

  1. Minced meat (nikakken nama)
  2. Kwai
  3. Attaruhu
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Curry
  7. Bread crumbs (garin biredi)
  8. Mai
  9. Tafarnuwa
  10. Ginger

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki dafa kwai sai ki bare ki ajjiye a gefe.

  2. 2

    Zaki gara attaruhu da albasa sai ki wanke kiyi grating dinsu.

  3. 3

    Saki sami kwana sai ki zuba nikakken nama aciki, sai ki kawo ginger da tafarnuwa wanda kika daka su

  4. 4

    Sai ki zuba aciki, sai kisa maggi, curry da attaruhu da albasa aciki sai ki juya,

  5. 5

    Sai ki dakko kwanki sai ki dinga dibar naman kina mannawa ajikin kwan ko ina da ko ina haka zakiyi ta yi har ki gama.

  6. 6

    Sai ki dakko scotch egg dinki kisashi acikin ruwan kwai sai ki cire kisashi acikin garin biredi sai kisa a mai ki soya,

  7. 7

    Amman wuta kadan ake sawa dan naman ya soyu idan aka cika wuta naman bazai soyu ba.

  8. 8

    Sai ki dakko kwai ki fasa acikin kwano mai kyau kisa gishiri kadan aciki sai ki juya sai ki daura mai akan wuta kisa wuta kadan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Aysher Babangida (Ayshert Cuisines)
rannar
Kano

Similar Recipes