Home Made Burger

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
Kano

Iyalina najin dadi sosae idan nayi musu biredi da kaena alokacin karin kumallo 😂😍hkan yasa koda yaushe bana rabo da gasa biredi kala kala❤😋

Home Made Burger

Iyalina najin dadi sosae idan nayi musu biredi da kaena alokacin karin kumallo 😂😍hkan yasa koda yaushe bana rabo da gasa biredi kala kala❤😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hour 15mins
4 yawan abinchi
  1. Kayan hadin biredin (burger bread);
  2. 1 cupfulawa (tsiri)
  3. 1 tbspsugar
  4. 1 tspmadarar gari
  5. 1 tspinstant yeast
  6. 1/2 tspgishiri
  7. 1kwae
  8. Halfcup madara mae dumi ko ruwa mae dumi
  9. 1and half tbsp butter
  10. Kayan hadin abin cikin biredin;
  11. Nikakken nama,kwae 1,attaruhu, danyar citta, tafarnuwa, sinadarin dandano, kayan kamshin girki da albasa
  12. Mayonnaise da ketchup
  13. Lettuce salad
  14. Tomatur
  15. Cucumber
  16. Albasa

Umarnin dafa abinci

1hour 15mins
  1. 1

    Ki tankade flour kisa sugar da madarar gari..

  2. 2

    Kisa yeast da gishiri ki juya..

  3. 3

    Saeki zuba ruwan kwae ki rage kadan na shafawa kafin a gasa,sannan ki zuba madara mae dumi ki kwaba

  4. 4

    Kisa butter kici gaba da kwabawa har sae yayi soft and smooth dough sannan ki rufe kisa a rana ko guri mae dumi y tashi na tsahon minti 30mins or 40mins

  5. 5

    Bayan y tashi saeki raba gida hudu kiyi balls dasu kisa a abin gashi,sannan ki shafa ragowar kwanmu a saman kisa cokali mae yatsu kiyi ado a saman kamar hka,sannan kisa a oven mae dumi ki gasa for 15mins or 20min at low heat..

  6. 6

    Nan ga abubuwan bukatarmu, zaki yanka tumatur, cucumber da albasa ki gyara ganyen salad dinki ki wanke,saeki zubawa nikakken namanki albasa, Citta, tafarnuwa da kika gogah attaruhu,kwae daya sinadarin dandano,dana karawa girki kamshi ki juya sosae su hade

  7. 7

    Sae mulmula balls hudu kisa mae kadan a kasko ki saka hadin naman ki danna yayi circle ki gasa both sides din har yayi sannan ki ajiye a gefe..

  8. 8

    Ki sami karamin kwano ki zuba mayonnaise da ketchup Ki juya sosae su hade,bayan biredin y gasu y huce tsafff saeki yanka biyu ki shafa hadin mayonnaise din a jikin kowane bari,sannan ki saka ganyen salad kamar hka

  9. 9

    Saeki dora naman akan ganyen salad din kisa albasa da cucumber kamar hka

  10. 10

    Saeki saka tumatur ki rufe da dayan murfin kamar hka,anan zaki iyah saka tsinken sakace a tsakiyar dan y zauna sosae...

  11. 11

    Sae kici da ruwan shayinki mae zafi☕😍😋

  12. 12

    Hmmmmm😋❤✔ dadi baa magana😂💃

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
rannar
Kano

sharhai (9)

Khadija Auwal
Khadija Auwal @cook_28480340
Tom yanxu idan baeta oven xae iya soyawa?

Similar Recipes