Rotti

Sadiya Taheer Girei
Sadiya Taheer Girei @cook_15214700
Bauchi

#SSMK malam bahaushe yace sai an gwada akan san na kwarai😋😋😋

Rotti

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#SSMK malam bahaushe yace sai an gwada akan san na kwarai😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya
rabin mudu
  1. Fulawa
  2. Madaran gari babban chokali nacin abinci daya
  3. chokaliBakin pawda rabin karamin
  4. Gishiri kadan
  5. Ruwa
  6. Kabeji guda daya
  7. Kokumba babba guda daya
  8. Tattasai
  9. Tumatur
  10. Attarugu guda biyu
  11. Albasa
  12. Mangyada
  13. Maggi star guda hudu
  14. Onga classic guda daya

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    Assalamu alaikum. Da farko wannan shine fulawana bayan na tankade shi

  2. 2

    Wannam kuma madarane a babban chokali sai bakin pawda da gishirin mu kadan duk na zuba a cikin fulawan na gauraya shi

  3. 3

    Nan kuma ruwa ne kofi daya na juye a ciki na fara kwabawa, da naga ruwan bazai isa ba saina sake kara kofi daya naci gaba da kwabawa har ya hadu yadda ake so

  4. 4

    Kamar yadda kuka ga kwabin da tauri ake yin shi kamar na taliyan murji, daga nan na kifa tirai na gutsuro kwabin ina murzawa da kwalba

  5. 5

    Saina samo kofi ina fitar da shep din rawun harna gama sannan nasa tukun suyana akan wuta na zuma mangada da man yayi zafi saina fara suya

  6. 6

    Bayan na gama suyan saina ajiye ahi gefe guda. Sannan na hado kayan miyana na gyara sannan na makadesu na dora akan wuta, kafin ruwan kayan miyan ya tsane sai na koma gyara kabeji na

  7. 7

    Na yanyan ka sannan na barbada gishiri na wanke tas na ajiye shi a gefe, nan kuma kokumba ce da maggi da ongan da zamu zuba a miyan mu, na yankan kokumban yan daidai

  8. 8

    Bayan ruwan kayan miyan ya tsane saina zuba mai na soya tare da zuba su maggi na gama saina sauke na dauko kabejina na juye akan miyan na gauraya ya hadu sosai

  9. 9

    Nan kuma soyayyen rotti nane

  10. 10

    Nan kuma gashi na fara zuba hadin kabejina akan ko wanni rotti

  11. 11

    Daga nan kuma saina zuba kokumbar daga saman kabejin, amma sai naga hakan bai min kyau a hoto ba shine na sake sabon jerawa a wani filetin sannan na dauki hoton😜

  12. 12

    Masha Allah😘ban san rotti na yayi dadi ba sai dana ga Mai gida da yarana suna wawa😅 sannan na ankara😋...

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sadiya Taheer Girei
Sadiya Taheer Girei @cook_15214700
rannar
Bauchi
I'm Sadiya Taheer based in Adamawa Married in Bauchi,i love cooking food also love to see others food and lean more too😍
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes