Alala

Zulaiha Adamu Musa
Zulaiha Adamu Musa @cook_36044083
Yobe State

Inason alala sosae akwae dadi 😋😋

Alala

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Inason alala sosae akwae dadi 😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake
  2. Mai
  3. Manja
  4. Attaruhu
  5. Tattasai
  6. Albasa
  7. Maggie
  8. Kayan dandano
  9. Yajin barkwano
  10. Leda(fara)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaka samu wakenka sae ka jika shi na yan wasu mintina

  2. 2

    Idan ya jika yanda hancinsa zae fita da wuri sae ka zuba a turmi ka surfa har sae kaga hancinsa ya fita

  3. 3

    Sae ka juye a roba ka zuba ruwa ka dunga wankewa kana tacewa a matsamin taliya har sae kaga hancinsa ya fita duka

  4. 4

    Sae ka zuba a roba ka zuba tattasai da albasa da attaruhu ka kai injin markade a markada maka yyi laushi Amma zaka iya markadawa a blander in tana markada wake

  5. 5

    In an markada maka sae ka zuba Maggie da sauran kayan dandano da Mai da manja da ruwan zafi amma ba Mai zafi sosae ba

  6. 6

    Sae ka juya shi sosae ka daura a Leda amma ba manya ba saboda in yyi manya cikinsa bazae dafu ba

  7. 7

    Inka gama daurawa sae ka zuba a tukunya ka zuba ruwa ka daura akan wuta kabarshi yyi ta dafuwa

  8. 8

    Idan ya dafu zakiga ya ciko tukunyar tana buduwa Kuma ya hade jikinsa

  9. 9

    Sae ki sauke ki zuba a plate ki yanka ki zuba Mai ko manja da yaji

  10. 10

    Shikenan alala ya kammala sae aci dadi lfy 😋😋😋

  11. 11

    Akarshe amfanin zuba ruwan zafi shine alalan ki zae hada jikinsa Kuma bazae yi kumfa ba inya dafu😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Zulaiha Adamu Musa
Zulaiha Adamu Musa @cook_36044083
rannar
Yobe State
inason girki sosae gaskiya💃💃💞💞💔💔
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes